Ka janye ka bar mani takarar bana –Nkeiruka Onyejeocha ta fadawa Gbajabiamila

Ka janye ka bar mani takarar bana –Nkeiruka Onyejeocha ta fadawa Gbajabiamila

Nkeiruka Onyejeocha, wanda ta ke wakiltar mutanen Mazabar Isuikwato da Umunneochi na jihar Abia a majalisar wakilan tarayya ta fito ta bayyana cewa tana neman takara a majalisa wannan karo.

Honarabul Nkeiruka Onyejeocha wanda ta ke majalisar tarayya tun 2007 ta bayyana muradun na ta ne kwanan nan kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Laraba 24 ga Watan Afrilu. Onyejeocha tana cikin manyan ‘yan majalisar APC

Nkeiruka Onyejeocha ta nemi Honarabul Femi Gbajabiamila wanda APC ta tsaida a matsayin ‘dan takararta a zaben majalisar wakilan na bana da ya hakura, ya janye mata. ‘Yar majalisar ta roki Gbajabiamila ya ajiye burinsa.

KU KARANTA: Buhari zai gana da Sanatocin APC masu neman takarar Majalisa

Ka janye ka bar mani takarar bana –Nkeiruka Onyejeocha ta fadawa Gbajabiamila

Nkeiruka Onyejeocha ta roki Femi Gbajabiamila ya janye mata takara
Source: UGC

Onyejeocha wanda za ta tafi majalisa a karo na hudu a 2019, tayi wannan kira ne a gaban ‘yan jarida lokacin da ta zanta da su a Garin Abuja. Onyejeocha take cewa abin da ya kamata shi ne a bar mutanen Ibo su fito da kakakin majalisa a 2019.

‘Yar majalisar take cewa ba za ta sabawa matakin da jam’iyyarsu ta APC ta dauka na tsaida Femi Gbajabiamila a matsayin ‘dan takararta a majalisar wakilai ba, amma ta nemi APC ta janye wannan yunkuri da ta ke yi, ta ba mace dama.

KU KARANTA: Zaben Majalisa na neman kawo wata baraka a cikin APC

Hon. N. Onyejeocha tace ya kamata a samu mace cikin manyan majalisar tarayya, sannan kuma tace tana ganin akwai bukatar APC ta tuna da mutanen Kudu da aka yi watsi da su wajen takarar majalisar a 2015 domin ayi wa kowa adalci.

A jawabin na ta, Onyejeocha ta bayyana cewa Abokin aikin na ta watau Gbajabiamila, mutumin kirki ne, amma ta nemi ya hakura da muradunsa ya duba Najeriya, ya hakura ya kyale mata wannan kujera saboda irin hidimar da tayi wa APC.

Daga cikin masu harin wannan kujera akwai Abdulrazak Namdas, Mukhtar Aliyu Betara, Idris Wase, Umar Bago, John Okafor, Babangida Ibrahim da kuma Honarabul Mohammed Gudaji Kazaure.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel