EFCC: Satar Biliyan 20 a UBEC ta jefa Turner a wajen EFCC

EFCC: Satar Biliyan 20 a UBEC ta jefa Turner a wajen EFCC

Mun ji cewa hukumar EFCC mai faman yakin da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a Najeriya tayi ram da wani wanda yake cikin manyan makusanta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kamar yadda labari yake zuwa mana, EFCC ta bi kama King Turner ta tsare ne da laifin cinye wasu makudan kudin kwangila. Ana zargin King Turner da yin sama da fadi da fiye da Niara Miliyan 240 na hukumar UBEC.

A cikin ‘yan kwanakin nan, Dakarun EFCC su ka kama Turner inda yake shan faman tambayoyi. Bayan haka kuma a cikin makon nan, jami’an hukumar sun dauke sa jirgi inda aka tsare sa da bincike a ofishin EFCC da ke Legas.

KU KARANTA:

EFCC: Satar Biliyan 20 a UBEC ta jefa Turner a wajen EFCC

King Turner ya shiga hannun Hukumar EFCC a Najeriya
Source: Original

Ana sa rai cewa a yau Laraba, 24 ga Watan Afrilu ne za a saki King Turner bayan ya sha matsa. Turner yana cikin manyan hukumar ta UBEC a lokacin mulkin PDP inda ake zargin wasu Biliyan 20 da bacewa a lokacin yana ofis.

Daga cikin wanda EFCC ta tsare akwai tsohon shugaban hukumar ta UBEC mai kula da harkar ilmin Boko a Najeriya, Mallam Suleiman Dikko. Ana zargin Dikko da wani ‘dan majalisa da yin aika-aika tsakanin 2012 zuwa 2014.

Binciken na EFCC ya nuna cewa an yi awon gaba ne da Naira Biliyan 20 daga asusun UBEC da niyyar cewa za a sayo kayan aikin gwaje-gwajen kimiyya a makarantun sakanadare 104 na gwamnatin tarayya a lokacin PDP na mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel