Mutan Jihar Borno, gobe ku sha baccinku ba aiki sakamakon ziyarar da Buhari zai kawo - Sanarwan Gwamnati

Mutan Jihar Borno, gobe ku sha baccinku ba aiki sakamakon ziyarar da Buhari zai kawo - Sanarwan Gwamnati

Gwamnatin jihar Borno ta alanta ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu matsayin ranar hutu saboda al'ummar jihar su fito kwansu da kwarkwatansu domin taraban shugaba Muhammadu Buhari da zai kawo ziyara jihar.

Wannan sanarwa ne da kwamishanan labaran jihar, Dakta Mohammed Bulama, yayi ranar Laraba inda yace: "Sakamakon ziyarar da mai girma shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kawo jihar Borno, gwamnatin jihar Borno ta alanta gobe, Alhamis, 25 ga watan Afrilu, 2019 matsayin ranar hutu."

"Saboda haka, muna kira ga al'umma su fito kwansu da kwarkwatansu domin tarban shugaban kasa da mukarrabansa."

"Gwamnati na mai bada hakuri kan duk wani rashin jin dadi da hakan zai kawo kuma ana bukatan fahimta da goyon bayan al'umma yayin wannan ziyaran."

KU KARANTA: Daya daga cikin jarirai biyar da matar jihar Kogi ta haifa ya mutu

Rahotanni sun suna cewa shugaban kasa zai tafi jihar Borno domin kaddamar da wasu manyan ayyukan gina-ginan makarantu da gidaje da gwamnatin jihar karkashin gwamna Kashin Shettima ta yi.

Mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kai jihar jihar Legas a yau Laraba, 24 ga watan Afrilu, 2019. A wannan ziyara ta musamman da shugaban kasan ya kai, ya kaddamar da wasu manyan ayyuka akalla hudu da gwamnatin gwamna Akinwumi Ambode ya kammala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel