Maigadi ya zabi a gina tuka-tuka a kauyensu a kan karbar kyautar gida

Maigadi ya zabi a gina tuka-tuka a kauyensu a kan karbar kyautar gida

Wani maigadi ya bukaci maigidansa ya rike kyuatar gidan da ya bashi a matsayin sallama tare da mika bukatar a haka rijiyar tuka-tuka a kauyensu.

Maigadin, Musa Usman, ya fito ne daga kauyen Giljimmi da ke karkashin karamar hukumar Birniwa a jihar Jigawa.

Wani dan asalin kasar Indiya ne ya so bawa Musa kyautar gida a matsayin sallamar aikin da ya dade yana yi masa a matsayin maigadi, amma sai ya nemi maigidan nasa ya gina musu rijiyar tuka-tuka a kauyensu.

Lamarin ya faru ne yayin da Musa zai dawo kauyensu bayan ya yi aiki a matsayin maigadin manajan kamfanin magunguna na 'Jawa International Limited' a jihar Legas na tsawon shekaru 25.

Manajan kamfanin, Mista V. Verghese, ya yanke shawarar gina wa Musa gida domin nuna jin dadin aikin da ya yi masa a matsayin maigadi.

Amma saboda matsanancin halin wuyar ruwa da kauyensu ke ciki, sai Musa ya nemi a bar maganar gina masa gida, a gina rijiyar tuka-tuka da jama'a zasu amfana.

Kafin ginin rijiyar da Musa ya nema a wurin maigidansa, mutanen kauyensa na yin tafiya mai nisan gaske kafin su samo ruwan sha mai tsafta.

A jawabinsa, Musa ya yi godiya ga Mista Verghese bisa aikin alherin da ya yi a kauyensu, ya ce ko kadan ba ya nadamar kin karbar kyautar gidan da ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel