Daya daga cikin jarirai biyar da matar jihar Kogi ta haifa ya mutu

Daya daga cikin jarirai biyar da matar jihar Kogi ta haifa ya mutu

Daya daga cikin yan biyar da aka haifa a babban asibitin FMC, Lokoja, jihar Kogi ranar 17 ga waaan Afrilu, 2019 ya mutu. shugabannin asibitin sun bayyana.

Diraktan cibiyar ayyuka na asibitin, Dakta Taiwa Jones, ya bayyanawa manema labarai cewa jaririn wanda ya kasance cikin kwalba tun lokacin da aka haifeshi ya mutu da safiyar ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu.

Da farko an haifi jaririn ta hanyar tiyata ne kuma nauyinsa ya kai kilo 1.3, hakan ya sa likitocin suka sanyashi cikin kwalba saboda ya yi karami da yawa.

Jones ya ce asibitin ta yi iyakan kokarinta na ganin cewa an ceci rayuwar yaron amma abin ya fi karfinsu.

Yace: "A lokacin haihuwar, hudu daga cikin yaran biyar sun fito lafiya kalau, amma na biyar din na da nauyin kilo 1.3 kuma bai da lafiya saboda wasu cututtuka. Shi yasa muka sanyashi cikin kwalba."

"Da farko mun yi tunanin cewa cutar jini ne amma abin ya kara tsanani har ya mutu ranar Litinin misalin karfe biyar na safe."

"Sauran yaran na nan cikin koshin lafiya. Za mu tabbatar da cewa sauran hudun da mahaifiyarsu suna da isasshen lafiya kafin a sallamesu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel