Najeriya da Ghana sun hada kai domin magance aikata miyagun laifuka ta hanyar yanar gizo

Najeriya da Ghana sun hada kai domin magance aikata miyagun laifuka ta hanyar yanar gizo

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta daura damarar hadin gwiwa da gwamnatin kasar Ghana domin magance aikata miyagun laifuka ta hanyar yanar gizo domin bunkasar ci gaba da kuma kyakkyawar alaka da ke tsakanin kasashen biyu.

Najeriya da Ghana za su hada kai domin magance aikata miyagun laifuka ta hanyar yanar gizo

Najeriya da Ghana za su hada kai domin magance aikata miyagun laifuka ta hanyar yanar gizo
Source: Depositphotos

Jakadan kasar Ghana zuwa Najeriya, Alhaji Bashir Bawa, shi ne ya bayar da shaidar hakan a ranar Laraba cikin birnin Calabar yayin ziyarar Kwanturola na hukumar shige da fice ta kasa a jihar Cross River, Mista Felix Uche.

Alhaji Bawa ya lura cewa hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki na kasashen biyu zai taimaka kwarai da aniyya tare da taka muhimmiyar rawar gani wajen magance miyagun laifuka da ake aikata wa ta hanyar yanar gizo da sauran ababe na sharri.

Ya ce bisa ga shimfida tsari da kyawawan dokoki wajen tarayya ta daura sulke a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, zai magance tare da kawo sauki na aukuwar miyagun laifuka kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Bayan ziyarar aiki a Legas, Buhari ya dawo garin Abuja

Jakadan na kasar Ghana ya yabawa hukumar shige da fice ta Najeriya sakamakon kyakkyawar dangantaka da ke ci gaba da habaka zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al'ummomin kasashen biyu da ke makotaka da juna a nahiyyar Afirka.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, gwamnatin kasar Ghana a watan Fabrairun da ya gabata ta taso keyar 'yan Najeriya kimanin 732 zuwa kasar su ta gado a sakamakon ci gaba da aukuwar miyagun laifuka ta hanyar yanar gizo da kuma karuwanci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel