An kawata birnin Maiduguri domin shirin tarbar Buhari

An kawata birnin Maiduguri domin shirin tarbar Buhari

-Kashim Shettima zai karbi bakuncin shugaba Buhari ranar Alhamis

-Birnin Maiduguri ya dauki sabon launi duk saboda ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari, inda zai kaddamar da manyan ayyuka guda 11

Babban birnin jihar Borno wato Maiduguri ya sha kwalliya iri daban-daban domin tarbar shugaba Muhammadu Buhari. An riga da an kammala dukkanin shirye-shirye saboda tahowar Buhari jihar a ranar Alhamis.

Shugaban kasa yayin ziyarar tasa dai, zai bude wasu ayyuka ne da gwamna Kashim Shettima yayi a cikin jihar.

An kawata birnin Maiduguri domin shirin tarbar Buhari

Shettima da Buhari
Source: UGC

KU KARANTA:Akan cin hanci da rashawa Buhari yayi dan kokari kadan, inji Wole Soyinka

Ayyukan da shugaban zai kaddamar sun shafi fannin lafiya, ilimi da kuma gidaje. Gaba daya manya-manyan ayyukan da shugaban kasar zai kaddamar guda 11 ne a cikin birnin na Maiduguri.

A yinin Laraba da wakilin jaridar THISDAY ya kewaya cikin babban birnin ya same shi tsaf, gwanin ban kaye. Tituna ma nan gwanin ban sha’awa sai sheki sukeyi.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta sheda mana cewa, mutanen gari su kasance cikin shiri domin wadansu hanyoyi zasu kasance a rufe lokacin ziyarar. Wannan zai kawo cikas musamman wurin zirga-zirga da ababen hawa.

Daga cikin ayyukan da za’a kaddamar sun hada da: jerin gidajen Njimtilo, jami’a mallakar gwamnatin jihar Borno, makarantun sakandare na zamani guda biyu, makarantar Aliko Dangote, aikin babban asibiti na sashen duba kirji da kuma titin bayan gari mai tsawon kilomita 10 na garin Pompomari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel