Cin kudin Atiku: PDP ta dakatar da shugaba da mataimakin jam'iyyar a jihar Filato

Cin kudin Atiku: PDP ta dakatar da shugaba da mataimakin jam'iyyar a jihar Filato

Jam'iyyar PDP a Filato ta sanar da dakatar da shugabanta na jihar, Honarabul Damishi Sango, da mataimakinsa, Amos Goyol, saboda badakalar kudi.

Sanarwar korar na kunshe a cikin wani jawabi da sakataren yada labaran jam'iyyar, John Akans, ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce: "bayan wani zama da zababbun shugabannin jam'iyyar PDP a jihar Filato suka yi ranar 24 ga watan Afrilu, 2019, domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi zabe da harkokin jam'iyya, mun yanke shawarar nuna rashin amincewar mu da shugabancin Honarabul Damishi da mataimakinsa, Honarabul Amos Goyol.

Cin kudin Atiku: PDP ta dakatar da shugaba da mataimakin jam'iyyar a jihar Filato

Atiku
Source: Facebook

"Domin kare mutuncin jam'iyyar mu, mun yanke shawara kamar haka: mun dakatar da shugaban mu Honarabul Dimishi Sango da mataimakinsa Amos Goyol. Mun dakatar da su ne bisa dalilai kamar haka; gaza bayyyana takamaiman adadin kudin da aka turo domin yakin neman zaben shugaban kasa, kin bayyana yadda aka kashe kudaden kamfen din shugaban kasa da kuma kirkirar fastocin kamfen ba tare da tuntubar ragowar shugabannin jam'iyya ba domin a fake da hakan wajen almubazzaranci da kudaden yakin neman zaben.

DUBA WANNAN: Fallasa: Wasu daga cikin aiyukan da Buhari zai kaddamar a Legas ba a kammala su ba

"Gaza yin bayanin yadda aka kashe kudin da jam'iyyar ta tara domin taimaka wa mazauna sansanin 'yan gudun hijira. Ya zama dole mu sanar da jama'a cewar mataimakin shugaban jam'iyya ne shugaban kwamitin tallafa wa 'yan sansanin gudun hijira. Hatta kudin gudanar wa na jam'iyya a jihar Filato sun gaza bayanin yadda aka kashe su.

Ragowar shugabannin sun zargi shugaban da mataimakinsa da canja sunan halastaccen dan takarar majalisar tarayya na jam'iyya a mazabar Wase da wani dan takarar ba tare da wani dalili ko tuntubar ragowar shugabannin njam'iyya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel