Bayan ziyarar aiki a Legas, Buhari ya dawo garin Abuja

Bayan ziyarar aiki a Legas, Buhari ya dawo garin Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo garin Abuja bayan ziyarar aiki ta yini guda da ya kai jihar Legas a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilun 2019. Shugaba Buhari ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka uku da ba bu makamancin su a duk fadin Najeriya.

Bayan kaddamar da muhimman ayyuka da gwamnatin jihar Legas karkashin jagorancin Gwamna AKinwunmi Ambode ta aiwatar, shugaban kasa Buhari tare da tawagar sa sun isa filin jirgin saman jihar da misalin karfe 3.00 na Yammacin Laraba.

Buhari yayin kaddamar da aiki a jihar Legas

Buhari yayin kaddamar da aiki a jihar Legas
Source: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, yayin barin filin jirgin saman kasa-da-kasa na Murtala Muhammad da ke birnin Legas, Buhari ya keta hazo cikin jirgin fadar shugaban kasa mai lamba 5N-FGT da misalin karfe 3.21 na Yamma.

Cikin wadanda su ka yiwa shugaba Buhari rakiya tare da sallamar barin garin sun hadar da; Gwamna Ambode na jihar, gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi, gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun da kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

Sauran tawagar da ta yiwa shugaba Buhari rakiya sun hadar da zababben gwamnan jihar Legas mai jiran gado, Mista Babajide Sanwo Olu da kuma mataimakin sa, Mista Obafemi Hamzat.

KARANTA KUMA: Asibitin koyarwa na Jami'ar Danfodiyo ya fara tiyata a zuciya

Akwai kuma kusoshin gwamnatin jihar da na gwamnatin tarayya da suka hadar da mambobin majalisar tarayya da na majalisar zantarwa da suka kasance tare da shugaban kasa Buhari yayin ziyarar sa ta yini guda.

Yayin ziyarar sa, shugaba Buhari ya kaddamar da sabuwar tashar Motocin haya ta Oshodi, sabuwar hanya a tashar jiragen sama da kuma wani sabon katafaren reshen lafiya na Yara da Mata mai cin gado 170 a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel