Gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 1000

Gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 1000

Gwamnatin jahar Kebbi zata kaddamar da shirin aikin tiyata a ido kyauta ga mutane dubu daya daga ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, kamar yadda gwamnan jahar, Alhaji Atiku Bagudu ya bayyana.

Gwamna Atiku Bagudu ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda yace gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da wannan aiki ne da hadin gwiwar kungiyar tallafi ta Musulunci, watau Islamic Relief Organisatio (IRO).

Gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 1000

Gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 1000
Source: Twitter

KU KARANTA; An kama wani Uba yana kokarin sayar da yaransa 2 akan kudi N350,000

Haka zalika Legit.ng ta ruwaito sanarwar ta kara da cewa za’a fara duba idanuwan marasa lafiyan daga ranar Alhamis a cibiyar kiwon lafiya ta Kalgo, dukkanin manyan Asibitocin kananan hukumomin jahar, da kuma cibiyar gwaje gwaje ta Medicaid dake Birnin Kebbi.

Har sai an duba idanun marasa lafiya kafin a kai ga yi masa ko ayi mata tiyata, don haka ake neman jama’a dasu bada hadin kai ga likitoci da sauran jami’an kiwon lafiya da zasu dubasu don samun nasarar aikin.

Gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 1000

Gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 1000
Source: Twitter

Manufar wannan aiki shine domin yaki da cutar makanta da sauran cututtukan ido a Najeriya gaba daya, don haka za’a fara tantance marasa lafiyan daga ranar 25 zuwa 19 ga watan Afrilu, sai kuma a fara yi musu aiki daga ranar 30 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Mayu.

Ga wasu lambobi da gwamnatin take kira ga jama’a su kira domin neman karin bayani game da aikin, wadannan lambobi sun hada da lambar Hafiz Bello; 08034068234 da kuma lambar Ruqayya Manga: 08064762624. Allah Yasa a dace, Amin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel