Majalisa ta daga tabbatar kasafin kudin wannan shekarar 2019

Majalisa ta daga tabbatar kasafin kudin wannan shekarar 2019

- Majalisar dattijai ta daga gabatar da kasafin kudi zuwa sati na sama saboda ba ta samu cikakken bayanai ba

- Majalisar ta bukaci a tattara duk wasu bayanai kafin ranar Litinin mai zuwa domin gabatar da kasafin kudi

A yau Larabar nan ne 24 ga watan Afrilu, majalisar dattijai ta kasa ta daga sanya hannu akan kasafin kudin shekarar 2019 zuwa mako mai zuwa saboda rashin samun cikakkun bayanai.

Kwamitin 'yan majalisun wanda Sanata Mohammed Danjuma Goje (APC Gombe) ya ke jagoranta, sun gabatar da kudurin kasafin kudin a ranar Alhamis din da ta gabata.

Majalisa ta daga sanya hannu a kasafin kudin wannan shekarar 2019
Majalisa ta daga sanya hannu a kasafin kudin wannan shekarar 2019
Source: Depositphotos

An wallafa yin la'akari da kasafin kudin da aka tsara a kan takardar majalisar dattijai a ranar Larabar nan.

Bayan haka kuma, lokacin da majalisar dattijan ta zauna akan maganar kasafin kudin, sun gano cewa babu cikakkun bayanai dangane da kasafin kudin.

KU KARANTA: Zamfara: Rundunar sojin sama ta yiwa 'yan bindigar jihar Zamfara luguden wuta

Sannan kuma sun lura cewa shugaban kwamitin Danjuma Goje da mataimakin sa Sanata Sunny Ogbouji (APC Ebonyi) ba su halarci zaman ba.

Amma babban dalilin jinkirta kasafin kudin shine rashin samun cikakkun bayanai.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya bukaci a tanadi bayanan kasafin kudin ga 'yan majalisar dattijai, kafin ranar Litinin, saboda majalisar ta sanya hannu a kai ranar Talata.

Ba wannan ne karo n farko da aka fara samun matsala a kan gabatar da kasafin kudi ba a kasar nan, musamman ma da hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kujera.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel