Yadda barayin motoci ke cin karensu ba babbaka a birnin tarayya Abuja

Yadda barayin motoci ke cin karensu ba babbaka a birnin tarayya Abuja

Biyo bayan hauhawa da aka samu wajen satar ababen hawa a wasu sassa na birnin Abuja da kewaye, anyi duba wa wasu sabbin hanyoyi da ake amfani dasu wajen aikata wadannan ta’asar.

Shahararriyar kasuwar Utako, wanda yayi kaurin suna wajen satar motoci, musamman ya kan kasance da cunkoso wanda hakan ke ba barayi dammar aiwatar da nufinsu cikin sauki.

Wani dan kasuwa a kasuwar, Mista Gabriel Francis, wanda ya zanta da majiyarmu, ya bayyana wasu dabaru da barayin motar ke amfani dasu.

Mista Fracis yace barayin na yawo a kewayen kasuwar a matsayin yan taxi ko masu siyayya, sannan da zaran wani da ya zo siyayya ya ajiye mota sai su nuna ra’ayinsu kan motar, daya daga cikinsu zai ta bibiyar mai motar yayinda zai ta ba sauran abokan ta’asar nasu bayani kan shige da ficen mai motar.

Yadda barayin motoci ke cin karensu ba babbaka a birnin tarayya Abuja

Yadda barayin motoci ke cin karensu ba babbaka a birnin tarayya Abuja
Source: UGC

“A haka, barawon motar zai yiwa sauran mambobin alama sannan su fasa motar da makuli sifaya sannan su tafi da motar,” inji shi.

Ya ci gaba da bayanin cewa motocin da ake sacewa a kasuwar sune wadanda ake fakawa akan hanya a wajen wurin ajiye motocin da aka kewaye.

Ya kara da cewa kwanan nan wani mutumi da matarsa sun ajiye mota a unguwar Ekukunam kusa da wajen ajiye motoci na kasuwa, sannan suka shiga shagon kasuwar, a lokacin da suka dawo basu tarar da motarsu ba an sace.

KU KARANTA KUMA: Takarar Bago ya hadu da cikas yayinda APC reshen Niger ta mara wa Gbajabiamila baya

Wani wajen sace mota shine a yankin kasuwar Amigo a Wuse II, Abuja.

Haka kuma a Garki, Area 11, yankin da ke tsakanin NTA da AGIS ana yawan samun cunkoso don haka cikin sauki barayin mota ke gudanar da ayyukansu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel