Akan cin hanci da rashawa Buhari yayi dan kokari kadan, inji Wole Soyinka

Akan cin hanci da rashawa Buhari yayi dan kokari kadan, inji Wole Soyinka

-Cin hanci da rashawa shi ke kawo cikas a fannin cigaban kasar nan, hakan ne yasa wannan gwamnati take tsaye akan kafafunta domin fada da cin hanci

-Ko yaushe matasa zasu samu ganin kasar da suka dade suna buri a Najeriya?

Shahararren marubucin turanci mai suna Farfesa Wole Soyinka shine yayi wannan kalami. Inda yake cewa duba ga halin da muke ciki ada da kuma na yanzu to ko shakka babu Shugaba Buhari ya kawo sauyi fannin yaki da cin hanci a kasar nan.

Soyinka yayi wannan batun ne yayin da yake tattaunawa a shirin “Hard Talk” na tashar BBC. Mafarkin da yan kasar nan ke dashi akan Najeriya har yanzu bai kasance ya zama gaskiya ba.

Akan cin hanci da rashawa Buhari yayi dan kokari kadan, inji Wole Soyinka

Buhari da Soyinka
Source: UGC

KU KARANTA:Kashi 80 cikin dari na ma’aikatan jihar Sakkwato na goyon bayanmu, inji Jagoran jam’iyar APC na jihar

Tambaya daga bakin Zeinab Badawi wacce ke gabatar shirin: “Shin kana ganin zamanin ku na dattajai kun gaza yiwa yan Najeriya abinda ya dace?

Soyinka: “Eh, tabbas hakane. Duba ga waccan lokacin da mukayi karatu a kasashen waje, yayinda muka dawo gida da niyyar cewa zamuyi iya bakin kokarinmu domin daga darajar kasarmu, ta yanda zata zarce takwarorinta na Afrika har duniya ma ta jinjina mata. Amma kash sai dai hakan bai samu ba.”

Yayinda yake sharhi akan zaben shugaban kasan daya gabata, yace: “Zaben 2019 shine zabe mafi damuwa da daure kai da muka taba samu a wannan kasa. Saboda a gani na, babu wani abu da mutum zai duba tsakanin yan takarar biyu (Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar) ta yanda zaka ce ai wani yafi wani daga cikinsu.”

“A zaben 2015, dole ce tasa aka zabi Buhari saboda mutane sun gaji da mulkin Jonathan don haka babu yanda za’ayi ya sake komawa kan mulki.”

Da yake magana akan lamarin cin hanci da rashawa ga abinda yake cewa, ko shakka babu shugaba Buhari ya cancanci yabo. Yayi kokari kadan na kawo sauyi a wannan bangare. A halin yanzu akwai mutane da dama wadanda suka hada da; tsofaffin gwamnoni, ma’aikatan banki, alkalai da ma wasu da dama suna gaban shari'a. Hakan zai karama matasa masu tasowa kwarin gwiwar ganin cewa kasar zata iya gyaruwa ko da nan gaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel