Ya kashe 'yan uwar budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi

Ya kashe 'yan uwar budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi

- Wani mutumi ya babbake 'yan uwan budurwarshi har lahira, saboda ta ce ta na so su rabu

- Mutumin ya yi amfani da man fetur da ashana ya sanyawa dakin da 'yan uwan budurwar ta shi suke ciki suna bacci wuta

A jiya Talata ne 23 ga watan Afrilu, 2019, ake zargin wani mutumi mai suna Deji Adenuga, wanda aka fi sani da suna Dakar, da laifin kunnawa 'yan uwan budurwarshi su takwas wuta a layin Adetuwo dake garin Igbodigo, cikin karamar hukumar Okitipupa, jihar Ondo.

Mun samu rahoton cewa mutane biyar daga cikin wanda aka sanyawa wutar sun mutu, inda sauran mutane ukun suke karbar magani a asibiti.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa Adenuga yana soyayya da wata budurwa wacce ke a gidan da abin ya shafa, mai suna Titi, amma daga baya ta zo ta ce bata son shi.

Ya kashe 'yan uwar budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi
Ya kashe 'yan uwar budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi
Source: UGC

Sanadiyyar rabuwar ta su ya saka wanda ake zargin sakawa dakin da 'yan uwan yarinyar guda takwas suke bacci wuta.

Majiyar ta ce, "Abinda ya faru yau Talatar nan da ban mamaki, saboda wani mutumi mai suna Adenuga ya kusa karar da dangin budurwarshi yau da safen nan.

"Ya na fushi, saboda yarinyar da yake soyayya da ita ta ce ba ta son shi. Saboda ya na son ya rama abinda yarinyar ta yi mishi sai ya watsawa dakin da iyalan yarinyar suke kwance suna bacci fetur ya cinna musu wuta.

KU KARANTA: 'Yan gari sun yi fito na fito da 'yan bindiga a jihar Katsina

"Sai dai cikin rashin sa a budurwar ta shi ba ta cikin dakin da ya sanyawa wutar.

"Mutane takwas daga cikin dangin yarinyar sun kone sosai, biyar daga cikin su sunce garinku nan, inda sauran uku da suka rage suke karbar magani a asibiti."

Majiyar ta bayyana cewa wanda ake zargin ya gudu ya bar garin jim kadan bayan ya kunna wutar, har yanzu kuma ba a san inda ya dosa ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan Jihar Ondo, Mista Femi Joseph, ya ce' yan sanda sun fara bincike akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel