Buhari ya samar da ayyuka miliyan 8 - Ngige

Buhari ya samar da ayyuka miliyan 8 - Ngige

Ministan kwadago da diban ma’aikata, Chris Ngige, ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samar da ayyuka miliyan takwas tun bayan da ya hau karagar mulki a 2015.

Ministan wanda yayi Magana a shirin Channels Television's Sunrise Daily a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu, yace samar da ayyuka ba hakkine na gwamnati ita kadai ba.

Legit.ng ta rahoto cewa ministan yace: “samar da aikinyi ba na gwamnati bane ita kadai. Ba a barwa gwamnati ita kadai. Mafi akasarin ayyuka da aka samar kamata yayi ya zama daga hukumomi masu zaman kansu.

Buhari ya samar da ayyuka miliyan 8 - Ngige
Buhari ya samar da ayyuka miliyan 8 - Ngige
Source: UGC

“Abunda muka gano lokacin da muka zo shine cewa tattalin arziki bai da kyau. Tattalin arziki inda ake siyar da mai kan $116 kowace ganga, ganga $2.2m a kowace rana tsawon shekari da dama amma babu tattali.”

KU KARANTA KUMA: An fara kaddamar da ayyuka yayinda Buhari ya isa Lagas

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mista Chris Ngige ya bayyana cewa bai damu da hukuncin likitoci wadanda suka zabi barin Najeriya ba don su yi aiki a kasashen waje.

Ngige wanda ya kasance bako a shirin Channels TV Sunrise Daily yace hakan ba sabon abu bane a Najeriya, saboda yan indiya ne suka karantar dashi a makarantar sakadare.

Da aka tambayi Ngige ko babu aibu, kasancewarsa likita kwararre, yace babu wani aibu a ra’ayinsu na aiki a kasashen waje.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel