Takarar Bago ya hadu da cikas yayinda APC reshen Niger ta mara wa Gbajabiamila baya

Takarar Bago ya hadu da cikas yayinda APC reshen Niger ta mara wa Gbajabiamila baya

Takarar Mohammed Bago (APC, Chanchaga) na Jihar Neja a matsayin kakakin majalisan wakilai ya gamu da cikas a ranar Litinin bayan yanke shawaran da jam’iyyar APC reshen jihar tayi na baiwa Gbajabiamila goyon baya.

Jam’iyyar APC a jihar Neja da mambobi takwas, tare da zababbun mambobin majalisar wakilai sun yanke shawaran goya ma dan takara Gbajiabiamila baya, bayan tattaunawa da aka gudanar a Gidan Gwamnati, da ke Minna.

Har ila yau dai mambobin sun nuna goyon bayansu ga dan takara Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Yayinda yake jawabi ga yan jarida a dakin tattaunawan da Gwamna Abubakar Sani Bello, shugaban jam’iyyar APC na jihar Neja, Engr Jibril Imam suka kira, sun ce jam’iyyar reshen jihar da mambobin majalisan dattawa daga jihar sun gaza saba ma shawarar shugabancin jam’iyyar na kasa akan wanda zai yi nasaran lashe shugabancin majalisa.

Takarar Bago ya hadu da cikas yayinda APC reshen Niger ta mara wa Gbajibiamila baya
Takarar Bago ya hadu da cikas yayinda APC reshen Niger ta mara wa Gbajibiamila baya
Source: UGC

Yace tattaunawan ya biyo bayan tattaunawan da dukkan shuwagabannin APC na jihohi da gwamnoni daga yankunan Arewa ta tsakiya da aka gudanar a Abuja.

KU KARANTA KUMA: An fara kaddamar da ayyuka yayinda Buhari ya isa Lagas

Yace taron na Minna ya samu halarcin mambobi shida daga jihar, yayin da sauran mambobi biyu suka nemi gafara akan rashin halarta amman sun yanke shawaran bin duk wata shawarar da aka yanke a taron.

Hon. Abdullahi Mahmud, mai wakiltan mazabar Agaei/Lapai a majalisar wakilai, wanda yayi magana a madadin sauran mambobi, yace shawarar tsayar da Lawan da Gbajiabiamila ya kasance matsayin shugabancin jam’iyyar, ya kara da cewa shawarar ta kasance tabbacin ikon jam’iyyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel