Gidauniyar Musulunci ta duniya ta gayyaci Sanata Wamakko taro a kasar Saudiya

Gidauniyar Musulunci ta duniya ta gayyaci Sanata Wamakko taro a kasar Saudiya

Gidauniyar musulunci ta duniya Muslim World League, ta gayyaci shugaban kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, zuwa wajen halartar taron ta da za ta gudanar cikin birnin Makkah a kasa mai tsarki.

Babban hadimi na musamman a kan hulda da al'umma na Sanata Wamakko, Alhaji Bashir Rabe Mani, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar Daily Trust.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko
Source: Twitter

Alhaji Rabe ya ce gayyatar Sanata Wamakko ta na kunshe cikin wata wasikar Gidanauniyar Musulunci ta duniya da sa hannun babban sakataren ta, Dakta Muhammad Bin Abdulkarim Al-Aisiy.

Cikin sanarwar da ya gabatar a birnin Shehu, Mani ya ce taron zai gudana ne a tsakanin ranar 14 zuwa 17 ga watan Ramalana na shekarar 1440 bayan hijirar Manzo Annabin tsira daga birnin Makka zuwa Madina wanda ya yi daidai da ranakun 19 zuwa 22 na watan Mayun 2019.

KARANTA KUMA: Kasar Saudiya ta zartarwa Mutane 37 hukuncin kisa

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Mai kula da Masallatai biyu mafiya alfarma a doron kasa na birnin Makka da kuma Madina, Sarki Salman Bin Abdulaziz As Saud na kasar Saudiya shi zai jagoranci taron da za gudanar cikin mafi alfarmar watanni.

A yayin da gwamnatin kasar Saudiya ke daukar nauyin kulawa da harkokin gidauniyar Musulunci ta duniya tun yayin kafuwar ta a shekarar 1962, hadimin Sanata Wamakko ya ce ana gina ta ne a kan tsari da akidu na da'awa da yada koyarwar addinin Islama.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel