Fallasa: Wasu daga cikin aiyukan da Buhari zai kaddamar a Legas ba a kammala su ba

Fallasa: Wasu daga cikin aiyukan da Buhari zai kaddamar a Legas ba a kammala su ba

A yain da shugaba Buhari ya isa jihar Legas domin ziyarar aiki ta kwana daya, jaridar Guardian ta fallasa cewar akwai aiyukan da basu kammalu ba daga cikin jerin aiyukan da gwamnatin jihar Legas ta ce shugaban kasar zai bude yayin ziyarar.

A ranar Talata ne Legit.ng ta kawo muku labarin cewar gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewar shirye-shirye sun yi nisa domin karbar bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda zai kai ziyarar aiki jihar ranar Laraba.

Ta ce yayin ziyarar ta kwana daya, shugaba Buhari zai kaddamar da wasu muhimman aiyuka a jihar.

"Daga cikin aiyukan da shugaban kasar zai kaddamar akwai hanya mai daukan motoci 10 a titin Oshodi/Murtala Mohammed da zai bulle har zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na jihar Legas da kuma wani dakin kwantar da marasa lafiya mai cin gado 170 da aka gina a sashen karbar haihuwa na asibitin koyar wa na jami'ar jihar Legasa, a Ikeja.

"Ragowar aiyukan sun hada da wani katafaren dakin taro mallakar jihar Legas da ke Ikeja, sabbin motocin jigilar mutane 820 da sauran su.

Fallasa: Wasu daga cikin aiyukan da Buhari zai kaddamar a Legas ba a kammala su ba

Daya daga cikin aiyukan da Buhari zai kaddamar a Legas
Source: Facebook

Sai dai, sabanin wannan sanarwa ta gwamnatin jihar Legas, rahoton jaridar Vanguard ya ce biyu daga cikin aiyukan da aka lisafa basu kammalu ba

"Sabanin sanarwar da gwamnatin jihar Legas ta fitar a kan aiyukan da shugaban kasa zai bude, hanya mai daukan motoci 10 da ta tashi daga Oshodi zuwa filin jirgin sama ba ta kammalu ba. An fara aikin tun shekarar 2017 amma har yanzu ko kusa da kammaluwa aikin bai yi ba." a cewar rahoton jaridar.

DUBA WANNAN: Buratai da shugabannin rundunar soji sun ziyarci fadar gwamnatin Kaduna

Rahoton ya kara da cewa har misalin karfe 8:00 na daren ranar Talata, an ga ma'aikatan kamfanin dake aikin hanyar na ta kokarin yin face-face a daidai karkashin wata gada a NAHCO/Toll Gate.

Kazalika, rahoton ya bayyana cewar ba kammala ko daya daga cikin gadojin tsallakawar jama'a da ke kan hanyar ba.

Sannan ta kara bayyana cewar akwai wani aikin hanya a Oshodi da aka bayar a kan kudi miliyan $70 tun shekarar 2016, wanda shi ma har yanzu bai kammalu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel