An fara kaddamar da ayyuka yayinda Buhari ya isa Lagas

An fara kaddamar da ayyuka yayinda Buhari ya isa Lagas

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu ya isa jihar Lagas don ziyarar aiki na kwana daya inda zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Akinwumi Ambode ta aiwatar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ra ruwaito cewa Buhari da tawagarsa sun sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, Lagas da misalin karfe 10:32am inda aka tsaurara tsaro.

Rahoton yace Shugaban kasar ya isa wajen a jirgin sojojin Najeriya mai lamba 5N-FGT sannan ya samu tarba da karramawa na mussamman.

An tattaro cewa daga cikin wadanda suka tarbi Shugaban kasar sun hada da Gwamna Akinwunmi Ambode na Lagas, takwaransa na Ondo, Abiola Ajimobi da Rotimi Akeredolu na jihar Ondo. Mataimakin gwamnan Edo, Phillip Shuaibu ma ya hallara.

An fara kaddamar da ayyuka yayinda Buhari ya isa Lagas

An fara kaddamar da ayyuka yayinda Buhari ya isa Lagas
Source: Twitter

Sauran wadanda suka tarbi Shugaban kasar a filin jirgin sun hada da zababben gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu, mataimakinsa, Obafemi Hamzat da manyan shugabannin tsaro.

NAN ta ruwaito cewa Buhari ya ziyarci Lagas, cibiyar kasuwancin Najeriya domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta gudanar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnati na za ta ci gaba da yiwa manoma kyakkyawar sakayya ta kwazon aiki - Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an zuba jami’an tsaro da dama a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagas gabannin ziyarar aiki da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa tuni jami’an tsaron suka kama bangarorinsu tun da misalin 7:15am. Jami’an tsaron sun hada da na rundunar sojin sama, hukumar kwastam na Najeriya, hukumar kula da shige da fice da kuma hukumar tsaro na NSCDC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel