Gwamnati na za ta ci gaba da yiwa manoma kyakkyawar sakayya ta kwazon aiki - Buhari

Gwamnati na za ta ci gaba da yiwa manoma kyakkyawar sakayya ta kwazon aiki - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan sanya manoma a mataki na mafi kololuwar karamaci, ya jaddada daurin damarar gwamnatin sa wajen ci gaba da yi masu kyakkyawar sakayya sakamakon kwazon su na aiki da jajircewa tukuru.

Cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya ce shugaban kasa Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Talata cikin fadar Villa yayin ganawa da mambobin gidauniyar tabbatar da ci gaban Najeriya mai tushe a kasar Birtaniya.

Gwamnati na za ta ci gaba da yiwa manoma kyakkyawar sakayya ta kwazon aiki - Buhari
Gwamnati na za ta ci gaba da yiwa manoma kyakkyawar sakayya ta kwazon aiki - Buhari
Source: Twitter

Domin tabbatar da kyautatawa manoma a Najeriya, shugaban kasa Buhari ya umurci babban bankin Najeiya da ya kawar da harkallar jingina wajen bai wa manoma damar karbar bashi cikin sauki da aminci.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya bayar da tabbacin tsayuwar dakan sa wajen yaki da fasakauri na shigo da kayan abinci cikin kasar nan daga kasashen ketare.

KARANTA KUMA: Kasar Saudiya ta zartarwa Mutane 37 hukuncin kisa

Kazalika shugaban kasar ya sha alwashin kara kaimi wajen inganta tsaro, habaka tattalin arziki, yaki da rashawa da kuma bunkasar harkokin ilimi da na lafiya a sabuwar gwamnatin sa cikin wa'adin ta na biyu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel