Likitoci na da ikon barin Najeriya saboda muna da rara, ban damu ba - Ngige

Likitoci na da ikon barin Najeriya saboda muna da rara, ban damu ba - Ngige

- Ministan kwadago, Mista Chris Ngige ya bayyana cewa bai damu da hukuncin likitoci wadanda suka zabi barin Najeriya ba don su yi aiki a kasashen waje

- Ngige yace hakan ba sabon abu bane a Najeriya, saboda yan indiya ne suka karantar dashi a makarantar sakadare

- Ministan yace akwai likitoci burjik a kasar don haka ba laifi bane don wasu sun zabi yin aiki a waje

Ministan kwadago da diban ma’aikata, Mista Chris Ngige ya bayyana cewa bai damu da hukuncin likitoci wadanda suka zabi barin Najeriya ba don su yi aiki a kasashen waje.

Ngige wanda ya kasance bako a shirin Channels TV Sunrise Daily yace hakan ba sabon abu bane a Najeriya, saboda yan indiya ne suka karantar dashi a makarantar sakadare.

“Ban damu ba, muna da rarar likitoci, idan muna da rara, muna fita dashi waje. Malamai yan indiya ne suka koyar dani wasu darusa a makarantar sakandare.

Likitoci na da ikon barin Najeriya saboda muna da rara, ban damu ba - Ngige

Likitoci na da ikon barin Najeriya saboda muna da rara, ban damu ba - Ngige
Source: Depositphotos

“Suna da yawa a kasarsu. Muna da rara a aikin likitanci a kasarmu. Zan iya fada maka wannan. A yankina, muna dasu da yawa. Muna da isassu, harma sunyi yawa, kuce ni na fada.”

Da aka tambayi Ngige ko babu aibu, kasancewarsa likita kwararre, yace babu wani aibu a ra’ayinsu na aiki a kasashen waje.

KU KARANTA KUMA: An tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Lagas gabannin ziyarar Buhari

“Babu wani aibu, sun je wasa basirarsu ne, su samu kudi sannan sun turo su gida. Kwarai, muna samun chanjin kudade daga garesu, ba wai daga mai ba.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel