An tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Lagas gabannin ziyarar Buhari

An tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Lagas gabannin ziyarar Buhari

An zuba jami’an tsaro da dama a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagas gabannin ziyarar aiki da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa tuni jami’an tsaron suka kama bangarorinsu tun da misalin 7:15am.

Jami’an tsaron sun hada da na rundunar sojin sama, hukumar kwastam na Najeriya, hukumar kula da shige da fice da kuma hukumar tsaro na NSCDC.

Har ila yau akwai jami’an hukumar kula da kare afkuwar hatsarurruka a kasa inda za su kula da kuma daidaita cunkoson ababen hawa a cikin filin jirgin da kewaye.

An tattaro cewa Buhari zai ziyarci Lagas, cibiyar kasuwancin Najeriya domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta gudanar.

KU KARANTA KUMA: Sanata Barau da Buba Galadima sun ja layi kan shugabancin majalisar dattawa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa sakamakon ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai zuwa jahar Legas a yau Laraba, 24 ga watan Afrilu, gwamnatin jahar Legas ta sanar da rufe wasu hanyoyi guda bakwai domin baiwa shugaban damar tafiye tafiye a garin ba tare da wata matsala ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ma’aikatar watsa labaru ta jahar Legas ta bayyana cewa ziyarar ta shugaba Buhari zata fara ne daga misalin karfe 9 na safiyar Laraba zuwa karfe 3 na rana, don haka za’a rufe hanyoyin a tsakanin lokacin nan.

A wannan ziyara ta musamman da shugaban kasan zai kai, zai kaddamar da wasu manyan ayyuka akalla hudu da gwamnatin gwamna Akinwumi Ambode ya kammala.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel