Kasar Saudiya ta zartarwa Mutane 37 hukuncin kisa

Kasar Saudiya ta zartarwa Mutane 37 hukuncin kisa

Gwamnatin kasar Saudiya ta tabbatar da zartuwar hukuncin kisa kan wasu Mutane 37 da su ka aikata laifuka daban-daban masu nasaba da ta'addanci kamar yadda Ministan harkokin cikin gida na kasar ya bayyana a ranar Talata.

Mutane 37 da su ka kasance 'yan asalin kasar Saudiya an zartar masu da hukuncin kisa sakamakon miyagun laifukan da suka aikata masu nasaba da ta'addanci kama daga ra'ayin rikau, kai hari tare da hallaka jami'an tsaro, da sauran dangin laifuka na ta'addanci.

Kasar Saudiya ta zartarwa Mutane 37 hukuncin kisa

Kasar Saudiya ta zartarwa Mutane 37 hukuncin kisa
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, cibiyar sadarwa ta kasar Saudiya ta kuma yi fashin baki kan laifukan da Mutanen su ka aikata na fasadi a ban kasa da kotun daukaka kara da kuma kotun koli na kasar su ka zartar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar yayin ganawa da manema labarai ya bayar da tabbacin cewa, gwamnatin Saudiya ba za ta sassautawa duk wadanda su ke da manufa ta kawo barazana ga zaman lafiya da kuma ci gaban kasar.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kasar Saudiya ta shahara wajen zartar da hukuncin kisa ta hanyar fille kai ko kuma a wani sa'ilin ta hanyar harbi da harsashi na bindiga a bainar al'umma.

KARANTA KUMA: Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin Afirka, Adesina

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Human Rights Watch, ta ce gwamnatin Saudiya ta zartar da hukuncin kisa kan mutane 139 a shekarar 2018 da ta gabata inda mafi akasarin laifukan da suka aikata su ka kasance na kisa da kuma laifuka masu nasaba da fataucin muggan kwayoyi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel