Ana rikicin cikin-gida a APC saboda kujerar Mataimakin Majalisar Dattawa

Ana rikicin cikin-gida a APC saboda kujerar Mataimakin Majalisar Dattawa

Rikicin cikin gidan da ake fama da ita a jam’iyyar APC mai mulki game da wadanda za su rike kujerun majalisar tarayya inda ake nema ayi wa shugaban APC bore a cikin manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar.

A Ranar 24 ga Afrilu, Jaridar The Sun ta rahoto cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar koli ta APC watau NWC, su na kokarin tuburewa matakin da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, ya dauka a kan raba kujerun shugabannin majalisa.

An samu rikici ne bayan da APC ta warewa yankin Kudu maso Kudu kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa, inda jam’iyyar ta ke so Sanatan ta na yankin Edo, Francis Alimekhena ya samu wannan mukami a majalisar tarayya.

Daily Sun ta samu labari cewa APC za ta tsaida Sanata Francis Alimekhena a matsayin mataimakin Sanata Ahmad Lawan. Francis Alimekhena ya fito ne daga jihar Edo, inda shugaban jam’iyyar ta APC, Adams Oshiomhole, yayi gwamna.

KU KARANTA: Buhari zai gana da Sanatocin APC masu neman kujerar Saraki

Ana rikicin cikin-gida a APC saboda kujerar Mataimakin Majalisar Dattawa

APC tana so Francis Alimekhena ya gaji Ike Ekweremadu
Source: Facebook

Sai dai wasu daga cikin manyan Sanatocin APC irin su Dr. Orji Uzor Kalu (APC, Abia); Ovie Omo-Agege (APC, Delta); Oluremi Tinubu (APC, Lagos); da kuma Sanata Kabiru Gaya (APC, Kano) su na harin wannan babbar kujera a majalisar dattawan.

Majiyar tace Mutanen yankin Kudu maso yamma na Ibo ba su ji dadin yadda ake neman hana su mataimakin shugaban majalisar dattawa a APC ba. Wannan ya sa har ta kai ana zargin Oshiomhole da yin abin da ya ga dama a tafiyar APC.

Rahotannin sun ce ana zargin Adams Oshiomhole da daukar mataki game da shugancin majalisar tarayya ta 9 ba tare da ya tuntubi majalisar zartarwa ta NEC da kuma majalisarsa ta NWC ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel