Mutane 19 sun mutu sanadiyyar hatsarin mota jihar Jigawa

Mutane 19 sun mutu sanadiyyar hatsarin mota jihar Jigawa

- Mutane 19 sun mutu sakamakon hadarin mota akan hanyarsu ta zuwa biki a jihar Jigawa

- Sai dai kuma cikin wani ikon Allah wani jariri ya rayu sakamakon jefo da mahaifiyarsa ta yi daga cikin motar

Rahotanni sun nuna cewa mutane goma sha tara ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya faru a karamar hukumar Gwaram cikin jihar Jigawa a jiya 23 ga watan Afrilun shekarar 2019.

An ce mutanen cikin motar sun kone kurmus, ta yadda ba a iya gane su, inda kadan daga cikin su, da jariri guda daya suka ji rauni.

Mun samu rahoton cewa jaririn ya kubuta ne, bayan da mahaifiyarsa ta jefo shi daga cikin motar a dai dai lokacin da lokacin da motar ta ke shirin faduwa.

Mutane 19 sun mutu sanadiyyar hatsarin mota jihar Jigawa

Mutane 19 sun mutu sanadiyyar hatsarin mota jihar Jigawa
Source: Depositphotos

Wani wanda lamarin ya faru a gabanshi ya bayyana cewa, motar mai dauke da kujeru 18 da lambar rijista KTG 245 YG, wacce ta taso daga garin Katagum za ta je Ningi cikin jihar Bauchi.

Rahotanni sun nuna cewa fasinjojin motar sun tashi daga garin Katagum dinne za su je garin Ningi biki, sai tayar motar ta fice, inda motar ta fadi ta kuma kama da wuta.

KU KARANTA: Zamfara: Rundunar sojin sama ta yiwa 'yan bindigar jihar Zamfara luguden wuta

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Jigawa, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya ce, har yanzu bai samu cikakken bayani dangane da lamarin ba.

Ranar Asabar din nan da ta gabata ne muka kawo muku rahoton yadda barayi su ka kashe wani limami a jihar Jigawa sannan suka dauke kudin gonar da ya sayar kimamin naira dubu dari hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel