'Yan Shi'a sun caccaki shugaba Buhari

'Yan Shi'a sun caccaki shugaba Buhari

- 'Yan Shi'a sun ce rundunar sojin Najeriya sun yi amfani da umarnin shugaba Buhari wurin kai wa shugabansu El-Zakzaky hari

- Sun kuma bayyana cewa ba su da wata alaka da gwamnatin tarayya dan haka baza su daina gabatar da zanga-zanga a kasar nan ba

'Yan kungiyar 'yan uwa musulmai, wadanda aka fi sani da 'yan shi'a, sun ci alwashin cigaba da gabatar da zanga-zanga akan rashin amincewa da gwamnatin tarayya ta yi da umarnin da kotu ta bayar na sakin jagoransu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenat.

Sheikh Zakzaky wanda hukumar tsaro ta farin kaya ta kama a shekarar 2015, ya yi bikin cika shekarunsa 68 a duniya a satin da ya gabata a gidan kurkuku.

'Yan Shi'a sun caccaki shugaba Buhari

'Yan Shi'a sun caccaki shugaba Buhari
Source: Facebook

Da ya ke magana da manema labarai jiya a Abuja, shugaban kwamitin yaki da fito da El-Zakzaky, Sheikh Abdulrahman Abubukar, ya ce: "Ba mu da wata alaka da gwamnati. Gaskiyar magana ita ce, bamu ji dadi ba akan cigaba da tsare shugaban mu da gwamnatin tarayya ta ke yi, duk kuwa da cewa kotu ta bayar da umarnin sakin shi.

"Mun yi imanin cewa sojoji sun kai wa shugaban na mu hari ne bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari."

KU KARANTA: 'Yan gari sun yi fito na fito da 'yan bindiga a jihar Katsina

"Duk kuwa da kotu ta bayar da cewa an tsare Sheikh ba bisa ka'ida ba, sannan kuma ta bayar da umarnin sakin shi, amma har yanzu gwamnati ta ki sakin shi, bayan sun san da cewa ba shi da lafiya. Hakan ne ya sa dole mu cigaba da bayyana ra'ayoyinmu dangane da abinda gwamnati tayi ta hanyar gabatar da zanga-zanga.

"Mun kai gwamnati kara zuwa kotu amma har yanzu ta ki bin umarnin kotu, saboda haka muna so 'yan Najeriya su zama alkalai akan wannan lamarin na El-Zakzaky. Dole ne mu tsaya domin bin hakkinmu."

Da aka tambaye shi ko kungiyar ta na da kudurin ware jiharta, Sheikh Abubakar ya jaddada cewa: "Babu wani mataki da muka dauka da ya ke nuna cewa muna so mu kafa jihar mu a kasar nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel