An kama wani Uba yana kokarin sayar da yaransa 2 akan kudi N350,000

An kama wani Uba yana kokarin sayar da yaransa 2 akan kudi N350,000

Wani mutumi mai shekaru talatin ya shiga hannu yayin da yayi kokarin sayar da yaransa guda biyu ga wani hamshakin attajirin dan kasuwa, akan kudi naira dubu dari uku da hamsin a jimlace, (N350,000) don ya tsira daga talauci.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutumin mai suna Edet Essien Inyang, mazaunin garin Calaba ta jahar Cross Rivers ya garzaya da yayan nasa ne zuwa titin Murray da zummar neman wanda zai saye yayan nasa, ta yadda zai samu saukin radadin talaucin da yake ciki.

KU KARANTA: Rundunar Sojan sama zata samu sabbin jiragen yaki guda 18 zuwa badi

Wani shaidan gani da ido mai suna Ekem ya bayyana cewa “Mutumin yazo nan tare da yaransa biyu yana tambayarmu gidan wani attajiri dake unguwarnan, amma bai samu ganin mutumin ba, sai muka tambayeshi mai zai ma mutumin.

“Anan ya kada baki yace wai yana neman wanda zai siya yayansa ne guda biyu, mace da namiji, namijin akan kudi naira dubu dari biyu (N200,000), macen kuma naira dubu dari da hamsin (N150,000), hakan ya bamu mamaki matuka.” Inji shi.

Mista Ekem tare da mutanen dake wurin sun yi ma Edet dabara, inda suka yi ta bata masa lokaci yayin da suke kokarin kira masa Yansanda, anyi sa’a sun samu Yansandan, inda suka aiko da jami’ansu suka kama shi, tare da garzayawa dashi zuwa ofishin Yansanda dake Atakpa.

Majiyarmu ta samu jin ta bakin DPO na Yansandan Atakpa, wanda ya tabbatar da kama mutumin, kuma yace tuni sun mika maganar zuwa ofishin binciken manyan miyagun laifuka dake shelkwatar Yansandan jahar don cigaba da bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel