Gwamnatin kasar China ta dauki nauyin zakakuran daliban ABU 48 don cigaba da karatu

Gwamnatin kasar China ta dauki nauyin zakakuran daliban ABU 48 don cigaba da karatu

Wasu zakakuran daliban jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria ta jahar Kaduna masu rike da kambun daraja ta daya a karatu, watau First Class, sun samu tallafin karo karatu daga gwamnatin kasar China, a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin kasar China tayi ma tallafin karatun taken ‘Oct 1st Scholarship for China-Nigeria friendship’, kuma ta mikashi ne ga shugaban jami’ar ABU ta hannun jakadan kasar China a Najeriya, Zhou Pingjiang, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Zhao Yong.

KU KARANTA: Rundunar Sojan sama zata samu sabbin jiragen yaki guda 18 zuwa badi

Gwamnatin kasar China ta dauki nauyin zakakura daliban ABU 48 don cigaba da karatu

Jami'ar ABU
Source: UGC

Zhao Yong yace akwai kyakkwa kuma dadaddiyyar alaka tsakanin kasar China da ABU, ya kara da cewa wannan shine karo na biyu da kasar China ke daukan nauyin daliban ABU zuwa kasarta don karo karatu.

“Kamar yadda kuka sani alakar Najeriya da China na cigaba da samun tagomashi, don haka jakadan kasar China, Dr Zhou Pingjiang ya kirkiro wannan tallafin karatu a matsayin sakayya ga hazikan dalibai a wasu jami’o’i, daga cikinsu har da ABU.

“An rada ma tallafin karatun taken ‘Oct 1st Scholarship for China-Nigeria friendship’ saboda ganin cewa Najeriya da China duk sun samu mulkin yancin kai ne a ranar 1 ga watan Oktoba, kuma tun shekarar 1971 alaka tsakanin Najeriya da China ta kulllu.” Inji shi.

Mataimakin jakadan ya kara da cewa kasar China ta kashe dala biliyan 2.8 a matsayin tallafi ga Najeriya wanda hakan ya samar da ayyukan yi ga yan kasa, tare da habbaka tattalin arziki, haka zalika huldar cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai dala biliyan 15.3 a 2018.

Da yake mika godiyarsa a madadin jami’ar ABU, shugaban jami’ar, Farfesa Ibrahim Garba ya jinjina ma kasar China, inda yace gudunmuwar da take baiwa jami’ar ba zai misaltu ba, haka zalika Farfesan ya bayyana cewa jakadan kasar China ya basu kyautan wani Malami dake koyar da harshen Chanis a ABU.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel