Rundunar Sojan sama zata samu sabbin jiragen yaki guda 18 zuwa badi

Rundunar Sojan sama zata samu sabbin jiragen yaki guda 18 zuwa badi

Rundunar mayakan Sojan sama ta sanar da cewa zata samu sabbin jiragen yaki guda goma sha takwas zuwa shekarar 2020 don kara yawan kayan aikin da take amfani dasu a kokarinta na kawar da duk wani barazanar tsaro a Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kwamitin bikin ranar rundunar Sojan saman Najeriya na shekarar 2019, Air Commdore Nnamdi Ananaba ne ya bayyana haka a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu yayin da yake ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Rikicin kabilanci: Mayakan rundunar Sojan kasa sun halaka Sojojin wata kabila a Benuwe

Daga cikin jiragen da rundunar dake tsimayin zuwansu Najeriya, akwai A-109 Power guda daya, Mi-35M guda daya, AW139 helicopter guda daya da kuma Super Tucano guda goma sha biyu.

“A cikin shekaru uku da suka gabata, rundunar sojan sama ta samu karin sabbin jiragen yaki guda goma sha shida da suka hada da Super Mushshak guda goma , Mi-35M guda hudu da Bell 412 helicopter guda biyu. Haka zalika mun tashi tsofaffin jirage goma sha hudu da suka hada da Falcon 900, ATR-42, Beechcraft, Super Puma, EC-135 Do-228, Mi-35P, F-7 da L-39.” Inji shi.

Da wannan ne Ananaba ke cewa an samu gagarumin cigaba a rundunar Sojan saman, wanda ya kamata su bayyana farin cikinsu bisa karin matsayi daga rundunar dake sakin bamabamai da hannu daga kan jirage a yakin basasa zuwa mallakar jiragen yaki na zamani masu sarrafa kansu.

“A yanzu haka mun samu sabbin matuka jiragen sama guda 90 a cikin shekaru uku da suka gabata, yayin da wasu guda 60 suke samun horo a ciki da wajen kasar nan, mun horas da sama da Sojoji 7,000, cikinsu har da dakaru na musamman guda 1000 da a yanzu suke bakin daga.” Inji shi.

Ana sa ran fara bikin ranar rundunar Sojan sama ne daga ranar 27 zuwa 29 ga watan Afrilu a babban birnin Abuja don murnar cikar rundunar shekaru hamsin da biyar (55) da kafuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel