Ziyarar Buhari zuwa Legas: Jerin manyan hanyoyi 7 da gwamnati zata rufe a yau

Ziyarar Buhari zuwa Legas: Jerin manyan hanyoyi 7 da gwamnati zata rufe a yau

Sakamakon ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai zuwa jahar Legas a yau Laraba, 24 ga watan Afrilu, gwamnatin jahar Legas ta sanar da garkame wasu hanyoyi guda bakwai domin baiwa shugaban damar tafiye tafiye a garin ba tare da wata matsala ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ma’aikatar watsa labaru ta jahar Legas ta bayyana cewa ziyarar ta shugaba Buhari zata fara ne daga misalin karfe 9 na safiyar Laraba zuwa karfe 3 na rana, don haka za’a rufe hanyoyin a tsakanin lokacin nan.

KU KARANTA: Atiku jikanmu ne, jininmu ne – Inji babbar masarautar jahar Jigawa

Ziyarar Buhari zuwa Legas: Jerin manyan hanyoyi 7 da gwamnati zata rufe a yau

Ziyarar Buhari zuwa Legas: Jerin manyan hanyoyi 7 da gwamnati zata rufe a yau
Source: UGC

Wadannan hanyoyi sun hada da titin Mobolaji Bank-Anthony, titin Kodesoh, titin Obafemi Awolowo, titin Kudirat Abiola, titin Ikorodu, babban titin Oworonshoki-Apapa, da kuma titin filin sauka da tashin jiragen jahar.

“Za’a rufe wadannan hanyoyin ne kawai idan bukatar hakan ta taso, amma titin Obafemi Awolowo da titin Bobolaji Banl-Anthony zasu kasance a rufe sakamakon sune manyan hanyoyin da shugaban kasa zai bi a yayin ziyarar.” Inji sanarwar.

Bugu da kari ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu manyan ayyukan more rayuwa da gwamnatin jahar Legas ta yi da suka hada da titin Oshodi/Murtala Muhammed Airport mai hannuwa 10, Asibitin Ayinke mai gado 170.

Sauran sun hada da babban dakin taro na jahar Legas a Ikeja, manyan motocin sufuri na gwamnati guda 820 da kuma wani katafaren hanyar motoci mai hawa uku dake Apapa-Oshodi.

Daga karshe sanarwar ta nemi hadin kan direbobi da masu ababen hawa don tabbatar da Buhari ya gudanar da wannan ziyara cikin kwanciyar hankali da lumana, sa’annan ta bayar da tabbacin jami’an tsaro zasu tabbatar kula da cunkoson ababen hawa akan sauran hanyoyin dake fadin jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel