Lawan ne ‘Dan takarar APC – Buhari zai fadawa Ndume da Goje

Lawan ne ‘Dan takarar APC – Buhari zai fadawa Ndume da Goje

Labari yana zuwa mana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zauna da manyan masu neman takarar shugaban majalisar dattawa a jam’iyyar APC a zaben da za ayi nan da ‘yan kwanaki kadan.

Shugaban kasar zai gana ne da Sanata Ahmed Lawan da kuma abokan hamayyar sa a APC watau Sanata Mohammed Danjuma Goje da kuma Mohammed Ali Ndume, a cigaba da kokarin da APC ta ke yi na hada kan ‘ya ‘yan ta.

Majiyar mu ta bayyana mana cewa Buhari yana shirin shiga tsakanin Sanatocin na APC da ke harin kujerar majalisar dattawa. Buhari zai bayyanawa Sanatocin jam’iyyar ta sa abin da ya sa APC ta zabi Ahmad Lawan yayi takara.

KU KARANTA: Shugaban Majalisar Wakilai yayi wa Tinubu wankin babban bargo

Lawan ne ‘Dan takarar APC – Buhari zai fadawa Ndume da Goje

Shugaban kasa zai sa baki a game da takarar Majalisar Dattawa
Source: Facebook

Masu neman kujerar ta Bukola Saraki a yanzu, su na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari bai fito ya nuna matsayarsa ba, wannan ya sa a wannan karo, tun wuri, zai zauna da manyan ‘Yan majalisar dattawan ya bayyana masu zabin sa.

Wannan zama zai taimaka wajen ganin gidan APC bai rabu wajen zaben shugaban majalisa ta 9 da za ayi idan an kafa sabuwar gwamnati ba. Ana tunanin cewa za ayi wannan zama ne daga yanzu zuwa cikin karshen makon nan da ake ciki.

Bayan an yi wannan zama daDanjuma Goje da Ali Ndume, APC za ta nemi ta ja layi domin ganin cewa ‘Ya ‘yan ta sun yi wa zabin da tayi biyayya na cewa Ahmad Lawan ne zai rike majalisar dattawan Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel