Enang, Akpabio, da Udoma sun sa Buhari ya rasa inda zai sa kan sa

Enang, Akpabio, da Udoma sun sa Buhari ya rasa inda zai sa kan sa

Yayin da kusan wata guda ya rage a cikin wa’adin farko na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, lissafin yadda za a bada mukamin Ministoci yana nema ya zamawa shugaban kasar ciwon-kai.

A Ranar 23 ga Afrilu, Vanguard ta rahoto cewa shugaba Muhammadu Buhari ya samu kan-sa cikin wani mawuyacin yanayi a game da wanda zai rike masa mukamin Minista daga jihar Akwa Ibom inda APC ke da manyan ‘yan siyasa.

A halin yanzu, shugaba Buhari yana da niyyar cigaba da aiki da Udoma Udo Udoma, wanda yayi kokari a ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare wajen ganin tattalin arzikin Najeriya ya fita daga cikin matslin lambar da ya shiga.

Duk da yadda Buhari yake son aiki da Udo Udoma, Ministan yana neman hanyar ajiye aiki a gwamnatin tarayya, bayan ya dade yana cikin gwamnati. Wannan ya sa Buhari ya karkata wajen Godswill Akpabio da kuma Ita Enang.

KU KARANTA: Shugaban Majalisa Dogara ya maidawa Jigon APC Tinubu martani

Enang, Akpabio, da Udoma sun sa Buhari ya rasa inda zai sa kan sa

Ita Enang da Akpabio sun sa Buhari cikin tsaka mai-wuya
Source: Depositphotos

Sanata Godswill Akpabio shi ne tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom wanda ya kuma sha kasa bayan yayi takarar Sanata a APC a zaben 2019. Akpabio kuma shi ne wanda yayi wa Buhari kokarin samun kuri’a masu tsoka a jihar ta sa.

Sai dai kuma shugaban kasar na tunanin inda zai cusa Sanata Ita Enang wanda yanzu haka shi ne ke bada shawara a kan harkokin ‘yan majalisa (na Dattawa). Yanzu dai ‘Yan adawa a Akwa-Ibom sun fi natsuwa da zabin Ita Enang.

Dokar kasa tace dole a zabi akalla Minista guda daga kowace jiha wanda hakan ba zai zo wa Buhari cikin sauki ba. A wani gefen kuma, Gwamnatin jihar Akwa Ibom ba za ta so shugaba Buhari ya ba Sanata Godswill Akpabio mukami ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel