Jagoranci mai inganci: Wamakko ya shawarci jam’iyun adawa

Jagoranci mai inganci: Wamakko ya shawarci jam’iyun adawa

-Jam'iyun adawa a jihar Sokoto sun shirya tsaf domin marawa gwamnati baya ta yanda za'a samu jagoranci mai inganci a jihar tasu

-Aliyu Wamakko, wanda yake jigone a siyasar Sokoto shine jagoran wannan tafiya

Yayinda hadakar jam’iyun adawa guda talatin suka kai masa gaisuwar ban girma da goyon baya, jagoran sanatocin arewa da kuma jigon jam’iyar APC a jihar Sokoto. Aliyu Wamakko ya shawarcesu dasu guji rashin aldalci kana kuma suyi bakin kokarinsu domin ganin an samar da gwamnati mai inganci a jihar.

Wamakko mai wakiltar Sokoto ta arewa, yayi wannan furucin ne yayinda hadakar jam’iyun suka ziyarce a gidanshi dake Sokoto. A matsayinmu na jam’iyun adawa a jihar nan, ya zama dole akanmu idan muka ga gwamnati tayi ba daidai ba mu jawo hankalinta domin ta dawo kan hanya.

Jagoranci mai inganci: Wamakko ya shawarci jam’iyun adawa

Sen. Aliyu Wamakko
Source: Twitter

KU KARANTA:Kazaman ‘Yan siyasa za su batawa Malamai suna – inji Sanata Shehu Sani

A cewarsa, hakan shi zai bada gwamnati mai ingnaci wanda za’aji dadinta a fadin jihar. Sanatan ya tabbatar musu da cewa a shirye yake da karbar shawara ko korafi daga wajensu, musamman idan ya shafi cigaban jihar Sokoto da ma kasa baki daya.

Shi kuwa a nashi jawabin mai magana da yawun wannan kungiya, Alhaji Mujittaba Aminu ya yabawa Wamakko inda yake cewa, “Mu a karskashin wannan kungiya tamu zamu cigaba da bashi goyon baya a siyasance. Wannan ya ta’allaka ne saboda mutum ne shi mai kishi da kuma tausayin jama’a.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel