A sirrance, a boye: An nada diyar Abba Kyari a matsayin mataimakiyar shugaba a hukumar NSIA

A sirrance, a boye: An nada diyar Abba Kyari a matsayin mataimakiyar shugaba a hukumar NSIA

An nada Aisha Abba Kyari, diyar shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Abba Kyari, a matsayin mataimakiyar shugabar hukumar kula da kudaden rarar man fetur da Najeriya ke samu daga sayar da danyen mai (NSIA).

An yi nadin ne cikin sirri, ba tare da sanarwa ko bin tsarin gwamnatin tarayya na daukan ma'aikata ko bayar da mukamin siyasa ba, kamar yadda wata majiya a hukumar NSIA ta sanar da majiyar mu.

Majiyar mu ta ce nadin Aisha ya saba wa hatta tanade-tanaden NSIA a matsayinta na hukuma da ke sarrafa kudaden shiga da Najeriya ta samu daga sayar da danyen man fetur.

A cewar majiyar NSIA; "babu inda aka tallata daukan aikin cike gurbin kujerar, sannan, ta kowacce fuska aka kalli abin, ba ta cancanta ba."

A sirrance, a boye: An nada diyar Abba Kyari a matsayin mataimakiyar shugaba a hukumar NSIA

Abba Kyari
Source: Depositphotos

A cewar jaridar TheScoop, Aisha tayi aiki ne na tsawon shekaru biyar kacal a wata hukumar gwamnati (National Integrated Power Project) kafin a nada ta a mukamin mataimakiyar shugaba a NSIA a watan Fabrairu, 2019.

DUBA WANNAN: Kuncin rayuwa: Wani mutum ya banka wa kan sa wuta bayan ya yi korafi da yunwa

Majiyar jaridar ta shaida mata cewar mafi karancin shekarun gogewa a aiki da ake bukata kafin a nada mutum a mukamin da aka bawa diyar Kyari shine shekara 10. Kujerar da aka nada Aisha, ita ce mafi girma a hukumar NSIA.

Aisha za ta karbi albashin miliyan N32 a shekara da karin wasu alawus. Tuni an ba ta sabuwar mota kamar yadda aka saba bawa jami'an hukumar da suka cika wata shida da aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel