JAMB: Makafi 390 suka zana jarabawar bana, an kama masu satar ansa 100

JAMB: Makafi 390 suka zana jarabawar bana, an kama masu satar ansa 100

Akalla makafi 390 ne suka zana jarabawar JAMB na bana wanda ta gudana a ranar 16 zuwa 17, 2019 a cibiyoyi hudu.

Wannan na kunshe ne a jaridar JAMB ta wannan mako na ranar 22 ga watan Afrilu, 2019 wanda shugaban hukumar sadarwa Dr Fabian Benjamin yasa hannu.

Bisa ga bayanin Jaridar, Makafi 57 ne a cikin 390 suka zana jarabawar a cibiyar Abuja, 59 a cibiyar Enugu, 135 a cibiyar kano sannan 139 a cibiyar Lagos.

A baya shugaban JAMB, Farfessa Ishaq Oloyede ya samar da wata kwamitin baiwa nakasassu dama tare da hadin gwiwar shugaban jami’ar NOUN kuma tsohon sakatare, farfesa Peter Okebukola, a shekarar 2017.

KU KARANTA: Wata mata ta farfado daga doguwar suma ta tsawon shekara 27

Kungiyar tana dauke da nauyin gudanar da jarabawar JAMB ga nakasassu saboda a tabbatar da cewa suma ba’a barsu a baya ba.

Okebukola ya yabawa shugaban JAMB ganin cewa ya taka rawar gani wurin taimakon nakasassu.

Har ila yau, Domin karfafa mutuncin hukumar a harkokin jarabawar, Jami’an tsaro sun kama masu satar amsa a akalla 100 a fadin kasar.

Cikin wadanda aka kama akwai wani wanda yayi rajista sau 64 akan zai zana ma mutane 64 tunda jarabawar ta gudana ne a cikin kwanaki 7 a zama 3 daga ko wacce cibiya.

Sannan an kama mutane biyu suna amfani da wayarsu wurin daukar hoton amsoshin jarabawar a wani gun registan jamb a Ikorodu jihar Lagos.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel