Kuskuren da Jonathan ya tafka ka ke maimaita wa - Wole Soyinka ya soki Buhari

Kuskuren da Jonathan ya tafka ka ke maimaita wa - Wole Soyinka ya soki Buhari

Fitaccen Farfesan Najeriya, Wole Soyinka, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yadda yake jan kafa wajen daukan mataki a kan aiyukan ta'addanci da makiyaya ke tafkwa wa a sassan kasar nan.

Ya ce Buhari ya gaza ta fuskar magance barazanar tsaro da makiyaya suka haddasa, ya kara da cewa shugaban kasar na maimaita kuskuren da tsohon shugaban kasa Jonathan ya tafka, na kin daukan matakan gaggawa a kan matsalar Boko Haram.

"Lalace wa tana tare da mutumin da ya yi shiru yayin da ake tafka barna," a cewar sa.

Soyinka na wadannan kalamai ne a ranar Litinin yayin da ya bayyana a shirin 'Hardtalk' na kafar yada labarai ta BBC.

Da yake amsa tambayar 'yar jaridar dake gabatar da shirin, Zainab Badawi, a kan goyon bayan Buhari da ya yi a shekarar 2015, Soyinka ya bayyana cewar babu yadda za a yi a wancan lokacin ya goyi bayan tsohon shugaban kasa Jonathan saboda irin cin hancin da ake tafka wa a gwamnatinsa baya ga rashin tsaro.

Kuskuren da Jonathan ya tafka ka ke maimaita wa - Wole Soyinka ya soki Buhari
Soyinka da Buhari
Source: UGC

Soyinka ya caccaki Jonathan a kan gazawar sa wajen magance matsalar Boko Haram, kazalika ya zargi tsohon shugaban kasa Obasanjo da barin kungiyar ta girma a lokacin da ya jagoranci Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007.

DUBA WANNAN: Mun kashe kaifin kungiyar Boko Haram - Gwamnatin Najeriya

A cewar sa; "Obasanjo ya taka rawa wajen kafuwar kungiyar Boko Haram ta hanyar gaza hana wani gwamna guda daya a arewacin Najeriya kaddamar da shari'ar Musulunci."

Soyinka ya kara da cewa Obasanjo ya kawar da kansa daga kan yunkurin gwamnan saboda kwadayinsa na son yin tazarce a kan karagar mulki.

Sai dai, Farfesan bai ce komai ba a kan abinda ya sa shugaba Buhari ya gaza daukan matakan magance matsalar tsaro da makiyaya ke haddasa wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel