Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi maraba da tayin da babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Gutters, ya yi masa na zama shugaba tare da shi a wani taro na kasa da kasa da za a yi domin neman kudi, biliyan $50 da za a yi amfani da su wajen farfado da tekun Chadi.
Shugaba Buhari ya samu takardar Guterres ne ta hannun shugaban bankin cigaban Afrika (ADB), Akinwumi Adesina, wanda ya ziyarci shugaban kasa a fadar sa ranar Talata.
Ta hannun Adesina ne shugaba Buhari ya fara aika takardar neman a gudanar da taro na musamman domin neman kudin da za a yi amfani da su wajen farfado da tekun Chadi ga Guterres.

Buhari da Guterres
Source: Twitter
Da yake karbar sakon amsar babban sakataren, shugaba Buhari ya ce akwai bukatar a gudanar da taro na musamman domin neman makudan kudaden da zasu bayar da damar sake jawo ruwa daga Afrika ta tsakiya domin farfado da tekun Chadi.
DUBA WANNAN: Aiyuka 6 da suka fi kawo kudi a Najeriya
Buhari ya bayyana cewar kasashen dake makobtaka da tekun Chadi ba zasu iya samar da kudaden da zasu farfado da tekun ba.
Da yake magana a kan nasarorin da bankin ADB ya samu, shugaba Buhari ya nuna farincikinsa a kan irin nasarorin da Adesina ya samu a cikin shekaru hudu da ya yi kan kujerar shugabancin bankin.
Shugaban kasar ya nuna gamsuwar sa a kan irin gudunmawar da bankin ADB ya bayar a bangaren bunkasa harkokin noma da aiyukan raya kasa a Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng