Kuncin rayuwa: Wani mutum ya banka wa kan sa wuta bayan ya yi korafi da yunwa

Kuncin rayuwa: Wani mutum ya banka wa kan sa wuta bayan ya yi korafi da yunwa

Rundunar 'yan sanda a jihar Ebonyi ta ce ta fara binciken mutuwar wani matashi matashi mai shekaru 37, Chinedu Nweze, wanda ya kashe kan sa saboda matsalar ciyar wa.

An garzaya da Nweze zuwa asibitin koyar wa na jami'ar Alex Ekwueme da ke Abakaliki domin ceto rayuwar sa bayan ya banka wa kansa wuta a bayan ajin makarantar firamare ta St. Patrik da ke unguwar Kpirikpiri, a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Rahotanni sun bayyana cewar Nweze ya daure kafafunsa kafin ya cinna wa kansa wuta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi, Lovett Odah, ya ce suna binciken lamarin domin tabbatar da gaskiyar cewar kashe kansa ya yi.

Kuncin rayuwa: Wani mutum ya banka wa kan sa wuta bayan ya yi korafi da yunwa

'Yan sandan Najeriya
Source: Depositphotos

Ana saura kwana daya ya aikata hakan, Nweze, dan asalin garin Umuogharu a karamar hukumar Ezza ta Arewa, ya yiwa makobtansa korafin cewar ya gaji da rayuwar fatara da rashi da suka sa ko ciyar da kansa ba ya iya yi.

DUBA WANNAN: Mun kashe kaifin kungiyar Boko Haram - Gwamnatin Najeriya

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan; "mun gaggauta aika motar daukan masu bukatar taimakon gagga wa zuwa wurin da abin ya faru bayan mun samu kira daga wani mutum.

"Yanzu haka muna kan gudanar da bincike a kan lamarin, ba mu samu isassun bayanan da zasu tabbatar mana da cewar kashe kansa ya yi ba, ko kuma wani abu ne daban ya faru ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel