Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin Afirka, Adesina

Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin Afirka, Adesina

Bayan ganawar sa ta sirrance da Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Sheikh Tamim bin Hamad Althani, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake kebancewa da shugaban bankin ci gaban Afirka AfDB, Akinwumi Adesina cikin fadar Villa da ke garin Abuja.

Adesina wanda ya kasance tsohon Ministan noma da raya karkara, ya iso fadar shugaban kasa da misalin karfe 2.45 na ranar Talata inda ba tare da wani tsaiko ba ya sakaya Labule tare da shugaban kasa Buhari.

Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin Afirka, Adesina
Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban bankin Afirka, Adesina
Source: UGC

Kawowa yanzu ba bu masaniyar dalilin ganawar manyan kasar biyu yayin da haka ta binciken manema labarai ba ta cimma ruwa ba kamar yadda kafar watsa labarai ta jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yayin zaman majalisar zantarwa da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata, gwamnatin tarayya ta yi amanna da karbar bashin Dalar Amurka miliyan 150 daga babban bankin AfDB domin yiwa sashen wutar lantarki garambawul a kasar nan.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na ganawar sirri da Sarkin Qatar a garin Abuja

Ministar kudi ta Najeriya, Hajiya Zainab Ahmed, yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa ta bayar da shaidar cewa, bashin da gwamnatin tarayya za ta karba ya yi daidai da kudirin ta na raya ci gaba karkara ta hanyar samar da wadatacciyar wutar lantarki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel