Gwamnatin jihar Legas ta kammala shirin karbar bakuncin Buhari ranar Laraba

Gwamnatin jihar Legas ta kammala shirin karbar bakuncin Buhari ranar Laraba

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana shirye-shirye sun yi nisa domin karbar bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda zai kai ziyarar aiki jihar ranar Laraba.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma'aikatar yada labarai a jihar Legas ta fitar ranar Talata.

Ta ce yayin ziyarar ta kwana daya, shugaba Buhari zai kaddamar da wasu muhimman aiyuka a jihar.

"Daga cikin aiyukan da shugaban kasar zai kaddamar akwai hanya mai daukan motoci 10 a titin Oshodi/Murtala Mohammed da zai bulle har zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na jihar Legas da kuma wani dakin kwantar da marasa lafiya mai cin gado 170 da aka gina a sashen karbar haihuwa na asibitin koyar wa na jami'ar jihar Legasa, a Ikeja.

"Ragowar aiyukan sun hada da wani katafaren dakin taro mallakar jihar Legas da ke Ikeja, sabbin motocin jigilar mutane 820 da sauran su.

Gwamnatin jihar Legas ta kammala shirin karbar bakuncin Buhari ranar Laraba

Ambode da Buhari
Source: Twitter

"Ziyarar ta shugaban kasa za ta fara ne daga karfe 9:00 na safe karfe 3:00 na ranar Laraba, za a rufe wasu hanyoyi na wucin gadi a tsakanin lokacin ziyarar," a cewar sanarwar.

Daga cikin hanyoyin da abin zai shafa akwai hanyar Moboloji zuwa Anthony da suke bullewa zuwa sashen saukar shugaban kasa na filin jirgin saman Legas, titin Kodesoh, titin Obafemi Awolowo, titin Kudirat Abiola da hanyar Ikorodu.

DUBA WANNAN: Kisan mutane fiye da 300: Wata kungiya ta dauki alhakin kai harin bam a Sri Lanka

A cikin sanarwar, gwamnatin jihar Legas ta shawarci masu ababen hawa da su kaurace wa amfani da hanyoyin da aka lissafa a sama.

Ta kara da cewa idan ya kama dole sai mutum ya yi amfani da daya daga cikin hanyoyin, to tilas ya kasance mai hakuri tare da yin biyayya ga ma'aikatan kula da cunkuson ababen hawa.

Kazalika, ta nemi hadin kan masu ababen hawa da sauran jama'a domin su kasance masu hakuri da yanayin da za su shiga na dan wani lokaci, ta kara da cewa akwai jami'an tsaro da ragowar ma'aikata a kowacce kusurwa a kan hanyoyin domin kula da motsin ababen hawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel