Shugabancin Majalisa: Buhari zai gana da zababbun gwamnonin APC

Shugabancin Majalisa: Buhari zai gana da zababbun gwamnonin APC

- Gwamnonin APC tare da shugaban jam'iyyar na kasa da kuma shugaban kasa Buhari za su gana a wannan mako kan batutuwan kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai

- Jam'iyyar APC ta kebance kujerar shugaban majalisar dattawa zuwa shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya

- Gwamnonin APC za su tattauna domin samun tabbacin goyon bayan 'yan majalisar wajen amincewa da kebance kujerar kakakin majalisar zuwa shiyyar Kudu maso Yamma

Cikin wannan mako ganawa za ta gudana tsakanin zababbun gwamnonin jam'iyyar APC reshen Arewa ta Tsakiya da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin amincewa kan wanda jam'iyyar za ta zaba a kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai.

Buhari yayin ganawa da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa

Buhari yayin ganawa da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa
Source: Facebook

Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa, ganawa za ta gudana tare da shugaban jam'iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole da kuma shugabannin jam'iyyar shida na rassan shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnoni da wasu jiga-jigan jam'iyyar yayin ganawa a ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu, sun shimfida goyon baya na kasancewar Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa da kuma Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai.

KARANTA KUMA: Rikici: Buhari ya bayar da umurnin kai agajin gaggawa jihar Taraba da Adamawa

A yayin da jam'iyyar APC ta kebance kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai zuwa shiyyar Arewa ta Tsakiya, rahotanni sun bayyana cewa, tuni gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya isa birnin Abuja domin tabbatar hadin kai a jam'iyyar na amincewa da hukuncin jam'iyyar na kebance kujerar majalisar wakilai zuwa shiyyar Kudu maso Yamma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel