Kisan mutane fiye da 300: Wata kungiya ta dauki alhakin kai harin bam a Sri Lanka

Kisan mutane fiye da 300: Wata kungiya ta dauki alhakin kai harin bam a Sri Lanka

Kungiyar addinin Islama (Islamis State) da aka fi kira da IS ta ce mambobinta ne suka kai harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mabiya addinin kirista a kasar Sri Lanka, kamar yadda kakakin kungiyar, Amaq, ya sanar.

"Wadanda suka kai harin kunar bakin wake a kan mabiya addinin kirista ranar Lahadi, mambobin kungiyar mu, ne" kamar yadda Amaq ya bayyana ranar Talata.

Sanarwar ta kara da cewa harin tamkar martani ne ga rundunar dakarun sojin kasar Amurka bisa cigaba da yaki da aiyukan kungiyar IS da suke yi a kasashen Iraq da Syria.

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin kunar bakin waken da aka kai Cocina da Otal-Otal a kasar Sri Lanka ya kai 321 a ranar Talata, kamar yadda hukumomi a kasar suka sanar.

Rundunar 'yan sanda ta ce adadin ya karu ne sakamakon mutuwar karin wasu mutanen da suka samu raunuka.

Kisan mutane fiye da 300: Wata kungiya ta dauki alhakin kai harin bam a Sri Lanka

Wata kungiya ta dauki alhakin kai harin bam a Sri Lanka
Source: UGC

A wata sanarwa da gwamnatin kasar Sri Lanka ta fitar, ta bakin mataimakin ministan tsaro, ta ce bincikenta ya nuna cewar masu kai harin sun aikata hakan ne a matsayin ramuwar gayya a kan harin da aka kai a kan wasu Masallatai a yankin Christchurch, a kasar New Zealand.

"Mun gamsu cewar kungiyar masu tsaurin akidar Islama ne suka kai harin a matsayin martani ga kisan Musulmai a Masallacin Christchurch a kasar New Zealand," a jawabin da Ruwan Wijewardene, ministan tsaro, ya gabatar a gaban majalisar kasar Sri Lanka.

DUBA WANNAN: Mu na nan daram a kan zargin da mu ke yiwa rundunar sojin sama - Sarakunan jihar Zamfara

Ministan ya kara da cewa; "kungiyar na da alaka mai karfi da wata kungiya da ake kira 'National Thowheed Jamath'. Dole mu dauki matakan gaggawa wajen haramta duk irin wadannan kungiyoyi masu tsauraran akidu."

An samu fashewar bama bamai yayin bikin Ista a wasu coci da ke Negombo, Batticaloa da Colombo da kuma wasu Otal guda uku a babban birnin kasar Sri Lanka.

An kama mutane 42 tare da gudanar da caje gidaje fiye da 20 a binciken kai harin da aka fara a kasar Sri Lanka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel