Rikicin kabilanci: Mayakan rundunar Sojan kasa sun halaka Sojojin wata kabila a Benuwe

Rikicin kabilanci: Mayakan rundunar Sojan kasa sun halaka Sojojin wata kabila a Benuwe

Dakarun rundunar Soja ta musamman ta 72 dake aikin tabbatar da tsaro a karamar hukumar Katsina Ala ta jahar Benuwe sun samu nasarar dakile aukuwar barkewar wani sabon rikicin kabilanci tsakanin kabilun tibabe guda biyu, Shitile da Ikyora a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan kasa, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, inda yace sun samu wannan nasara ne bayan samun wasu bayanan sirri dake nuna Sojojin kabilar Shitile sun kwaso jiki da nufin kai ma jama’an kabilar Ikyora hari.

Rikicin kabilanci: Mayakan rundunar Sojan kasa sun halaka Sojojin wata kabila a Benuwe

Makamansu
Source: Facebook

KU KARANTA: Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yan bindiga sun yi awon gaba da Matan aure 9 a jahar Neja

Wannan ne yasa Sojojin suka shirya ma yan bindigan harin kwantan bauna akan hanyar da suke tsammanin yan bindigan zasu biyo, inda suka taresu, suka kuma yi musu luguden wuta, nan take suka kashe yan bindiga biyar.

Wasu daga cikin kayayyakin da Sojojin suka kwato sun hada da bindigar AK 47 guda biyu, motoci biyu, babura bakwai, alburusai da dama da wata bindigar harba bamabamai guda 1.

Rikicin kabilanci: Mayakan rundunar Sojan kasa sun halaka Sojojin wata kabila a Benuwe

Ababen hawansu
Source: UGC

Daga karshe rundunar tana mika godiyarta da duk wadanda suka bata bayanan sirrin da suka kaita ga samun wannan babbar nasara, sa’annan rundunar na kira ga jama’a dasu kasance masu kaunar junansu, kuma su gaggauta kai bayanai game da take taken duk mutumin da basu gane mai ga hukumar tsaro don daukan mataki.

A wani labarin kuma mukaddashin gwamnan jahar Benuwe, Abouno ya kaddamar da dokar ta baci a garin Katsina Ala na jahar Benuwe sakamakon wani hari da wasu miyagu suka kaddamar a ranar Lahadi a garin.

Wannan hari da miyagun yan bindiga suka kaddamar a kauyukan Katsina Ala da suka hada da Ngibo da Tse-Aye yayi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha daya, sa’annan suka yi garkuwa da mutane biyar, tare da sace shanu 28 da kuma kona gidajen jama’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel