Rikici: Buhari ya bayar da umurnin kai agajin gaggawa jihar Taraba da Adamawa

Rikici: Buhari ya bayar da umurnin kai agajin gaggawa jihar Taraba da Adamawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin kai agajin gaggawa kan al'ummomin da rikici a kwana-kwanan nan ya ritsa da su cikin jihohin Adamawa da kuma Taraba kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, tawagar kai agajin ta sauka cikin birnin Yola a ranar Litinin bisa jagorancin Air Commodore Akube Iyawu, wanda ya kasance jagoran lalube da ceto na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA.

Iyawu cikin fadar Hamman Bata da fadar Hamman Bachama na garin Demsa da kuma Numan, ya ce tawagar sa ta kawo ziyarar da manufa daya da ta kasance kiyasi da kuma aune girman barna ta salwantar rayuka da kuma dukiya da rikicin ya haifar.

Rikici: Buhari ya bayar da umurnin kai agajin gaggawa jihar Taraba da Adamawa

Rikici: Buhari ya bayar da umurnin kai agajin gaggawa jihar Taraba da Adamawa
Source: Depositphotos

A yayin bayar da shaidar kai ziyarar su bisa ga umurni na shugaban kasa Buhari, Iyawu ya ce shugaban kasar na kuma mika sakon sa na ta'aziyya da jajantawa wadanda mummunan tsautsayin ya ritsa da su.

Jagoran tawagar yace, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari, za ta bayar da agajin gaggawa nan ba da jimawa ba kan al'ummomin da ibtila'in ya afkawa domin saukaka masu radadin bakin ciki da ke tare da su a yanzu.

KARANTA KUMA: Gwamnoni, Ministoci na neman samun shiga a sabuwar Majalisar Buhari

Rikicin al'umma da ya auku cikin kauyen Bolon na karamar hukumar Demsa, ya salwantar da rayukan mutane hudu yayin da Mutane 10 su ka raunata kamar yadda shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Adamawa ya bayyana, Dakta Muhammad Sulaiman.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel