Gwamnoni, Ministoci na neman samun shiga a sabuwar Majalisar Buhari

Gwamnoni, Ministoci na neman samun shiga a sabuwar Majalisar Buhari

A yayin ci gaba da karatowar ranar rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a sabon wa'adin sa na biyu, da yawa daga cikin makarraban sa na ci gaba da fafutikar neman samun shiga a sabuwar Majalisar sa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, wani tsohon ma'aikacin dakarun soji, gwamnoni uku masu barin gado da kuma Ministoci 15 na ci gaba da hankoron samun madafar iko a sabuwar majalisar shugaban kasa Buhari.

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar sabuwar gwamnatin shugaban kasa Buhari a wa'adin ta na biyu, za ta kebance kujerar sakataren gwamnatin tarayya zuwa ga shiyyar Arewa ta Tsakiya musamman kuma ga mabiyin addinin Kirista na yankin.

Gwamnoni, Ministoci na neman samun shiga a sabuwar Majalisar Buhari

Gwamnoni, Ministoci na neman samun shiga a sabuwar Majalisar Buhari
Source: Facebook

Bayan haka kuma shugaban kasa Buhari na ci gaba da fuskantar matsin lamba ta nadin mukamai 42 a sabuwar Majalisar sa domin tabbatar da kudiri da kuma manufa ta tafiyar da kowa da kowa cikin sabuwar gwamnatin sa.

Cikin sabon tsarin Majalisa da ake sa ran shugaba Buhari zai yi amanna da ita, za ta hadar da Ministoci 36 inda ko wace jiha dake fadin Najeriya za ta samar da guda daya. Kazalika Majalisar za ta yi nadin mukami ga ko wane wakili daya daga shiyoyi shidda na Najeriya.

KARANTA KUMA: Ba bu mai iya yiwa Majalisar tarayya kutse wajen zaben shugabannin ta - Saraki ya yiwa Tinubu raddi

A yayin da Mata, Ministoci da kuma gwamnoni masu barin gado ke ci gaba da fafutikar neman samun shiga a sabuwar majalisar shugaban kasa Buhari, kawowa yanzu shugaban kasar bai fadi hukuncin sa ba a kan nadin mukamai 42 kamar yadda jaridar Legit.ng ta fahimta.

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, ba bu lallai shugaban kasa Buhari ya sauya mai rike da kujerar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari a sakamakon cikakken yakini na aminci da kuma yarda da ke tsakanin su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel