Ba bu mai iya yiwa Majalisar tarayya kutse wajen zaben shugabannin ta - Saraki ya yiwa Tinubu raddi

Ba bu mai iya yiwa Majalisar tarayya kutse wajen zaben shugabannin ta - Saraki ya yiwa Tinubu raddi

Abubakar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa da zai bar gado a kwana-kwanan nan baya shan kaye yayin zaben kujerar Sanatan shiyyar Kwara ta Arewa, ya yiwa jigon APC Bola Tinubu raddin kan wanda zai maye gurbin sa.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Dakta Bukola Saraki, a ranar Litinin din da ta gabata ya karkarewa tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu da sauran kusoshi na jam'iyyar APC kan yadda jagoranci zai kasance a sabuwar Majalisar tarayya.

Shugaban Majalisar dattawa; Bukola Saraki tare da kakakin majalisar wakilai; Yakubu Dogara

Shugaban Majalisar dattawa; Bukola Saraki tare da kakakin majalisar wakilai; Yakubu Dogara
Source: Facebook

Saraki ya ce hakar Tinubu da dukkanin makarraban sa na yin kutse wajen zaben shugabannin majalisar tarayya ba za ta cimma ruwa ba kamar yadda su ka sha mamaki da kuma kunyar gaske a watan Yuni na shekarar 2015.

Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, Saraki cikin wani furuci da sanadin hadimin sa na sadarwa, Alhaji Yusuph Olaniyoni, ya mayar da martani zuwa ga Tinubu inda a ranar Lahadin da ta gabata ya kalubalanci jagorancin sa da cewar ya yiwa kujerar sa rikon sakainar kashi.

A sakamakon takkadamar dasa wani hasafin dukiya na bogi cikin kasafin kudin kasa na baya, Tinubu ya ce rikon sakainar kashi ta jagorancin majalisar tarayya ce ta haddasa wannan abin kunya a kasar nan.

KARANTA KUMA: Har yanzu ba mu saki sakamakon jarrabawar bana ba - JAMB

Saraki yayin barrantar da wannan zargi daga kan majalisar dattawa da cewa nauyin shigar da kasafin kasa cikin doka bai takaita kadai akan majalisar tarayya ba, ya ce nauyin ya hadar da fadar shugaban kasa.

Da ya ke jaddada maimacin shan kunya a kan Tinubu, Saraki ya ce hakar sa ta yunkurin kafa shugabanni a sabuwar majalisar tarayya ta bana ba za ta cimma ruwa ba kamar yadda ta kasance a shekarar 2015.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel