Har yanzu ba mu saki sakamakon jarrabawar bana ba - JAMB

Har yanzu ba mu saki sakamakon jarrabawar bana ba - JAMB

Hukumar gudanar da jarrabawar neman shiga jami'a a Najeriya JAMB, ta ce nan ba da jimawa ba za ta sadar da sakonni zuwa ga dalibai domin sanar da su a kan lokacin da za ta saki sakamakon jarrabawar ta da a ka gudanar a bana.

Kamar yadda jaridar Premium Times ya ruwaito, hukumar JAMB ta ce a kwana-kwanan nan za ta tura sakonnin tas ga dalibai masu neman shiga jami'o'i domin sanar da su a kan lokacin da za ta saki sakamakon jarrabawar bana da zarar ta kammala tantancewa.

Shugaban cibiyar sadarwa na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata hira yayin ganawar sa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai a ranar Lahadi cikin birnin Legas.

Har yanzu ba mu saki sakamakon jarrabawar bana ba - JAMB

Har yanzu ba mu saki sakamakon jarrabawar bana ba - JAMB
Source: Depositphotos

A cewar sa, Dakta Benjamin ya nemi dalibai da su kauracewa sauraron jita-jitar masu yada kanzon kurege da rade-radi marasa tushe a kan sakamakon jarrabawar bana musamman a kafofi da dandalan sada zumunta.

KARANTA KUMA: Bikin Easter: An hallaka Matasa 11 a jihar Gombe

Rahotanni sun bayyana cewa, fiye da dalibai miliyan 1.8 masu neman shiga jami'a a Najeriya sun zana jarrabawar JAMB ta bana cikin dukkanin jihohi da ke fadin kasar nan a tsakanin ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu zuwa ranar Laraba, 18 ga watan Afrilun 2019.

Hukumar JAMB bisa jagorancin Farfesa Ishaq Oloyede, ta yaba da salo, tsari da kuma yanayi na gudanar da jarrabawar bana da a cewar ta wannan karo ta tsarkaka daga ababe na magudi ko kuma kalubale sabanin yadda ta fuskanta a baya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel