Bikin Easter: An hallaka Matasa 11 a jihar Gombe

Bikin Easter: An hallaka Matasa 11 a jihar Gombe

Da sanadin kafar watsa labarai ta jaridar Daily Nigerian mun samu rahoton cewa, kimanin rayukan Matasa 11 sun halaka a wani mummunan hatsari mota da ya auku da sanyin safiyar ranar Litinin a jihar Gombe.

Rahotanni sun bayyana cewa, ajali ya ritsa da wasu Matasa 11 mabiya addinin Kisrista yayin aukuwar wani mummunan hatsarin Mota a ranar Litinin ana tsaka da gudanar da shagulgula na bikin Easter a jihar Gombe.

Bikin Easter: An hallaka Matasa 11 a jihar Gombe
Bikin Easter: An hallaka Matasa 11 a jihar Gombe
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hatsarin ya auku ne yayin da wata Mota da ta sharo hanya ta mutsuttsuke Matasan su na tsaka da gudanar da tattakin bikin Easter na mabiya addinin Kirista a jihar Gombe.

Shugaban cibiyar lafiya ta jihar Gombe, Dakta Shu'aibu Mu'azu, ya bayar da shaidar cewa an killace gawawwakin Mutane takwas da misalin karfe 1.00 na daren Litinin inda daga bisani aka garzayo da wasu gawawwakin na Mutane uku da suka riga mu gidan gaskiya.

Dakta Mu'azu ya ce ana ci gaba da kulawa da wadanda su ka raunata a yayin aukuwar tsautsayin a cikin asibitoci da dama na birnin Gombe da su ka hadar da na kudi da kuma gwamnati.

KARANTA KUMA: Bayan hutun 'Easter' za mu saki sakamakon jarrabawa - JAMB

Mashaida wannan mugun ji da mugun gani sun bayar da shaidar cewa direban Motar mai lamba AS 385 GME ya kasance jami'i na hukumar kula da al'umma ta NSCDC, Adamu Abubakar.

Kwamandan hukumar kiyaye aukuwar hadurra reshen jihar Gombe, Dakta Godwin Omiko, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan mummunan tsautsayi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel