Gwamnatin tarayya ta hukunta duk ma’aikatar da ta ki biyan N30,000 mafi karancin albashi – Balarabe Musa

Gwamnatin tarayya ta hukunta duk ma’aikatar da ta ki biyan N30,000 mafi karancin albashi – Balarabe Musa

Balarabe Musa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta kare ma’aikata a kasar ta hanyar hukunta duk ma’aikatar kwadago da ta ki amincewa da biya N30,000 na sabon mafi karancin albashi wanda ya samu goyon bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku tuna cewa shugaba Buhari ya sanya hannu a dokar mafi karancin albashi n 2019 a ranar 18 ga watan Afrilu.

Dokar ta bukaci dukkan in ma’aikatar kwadago a fadin kasar da ta biya ma’aikata mafi karancin albashi na 30,000 duk wata.

Da yake Magana a wata hira da jaridar Daily Independent, Musa wanda ya yaba ma shugaba Buhari akan sanya hannu a dokar sabon albashin, yace duk wata ma’aikata da ta ki biyan karancin albashin, kada a barta ta ci bulus.

Gwamnatin tarayya ta hukunta duk ma’aikatar da ta ki biyan N30,000 mafi karancin albashi – Balarabe Musa

Gwamnatin tarayya ta hukunta duk ma’aikatar da ta ki biyan N30,000 mafi karancin albashi – Balarabe Musa
Source: UGC

Yace: “Bara mu yaba ma gwamnati, akalla dai ta saurara kuma tayi abunda ya kamata akan sabon karancin albashi amma kuma ta kwana da sanin cewa tunda ta dauki dogon lokaci kafin amincewa da dokar, kididdiga ya nuna cewa albashin N30,000 duk wata yayi kankantar da zai dauke matsalolin ma’aikaci mai karamin karfi.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Dalilin da yasa nake goyon bayan Lawan da Gbajabiamila – Tinubu

“Har yanzu da akwai sauran matsala. Yanzu da aka amince da dokar, Shugaban kasar ya tabbatar da cewar an hukunta duk ma’aikata da ta ki biyan karancin albashin; saboda idan muka amince dashi kawai sannan muka ki kare ma’aikata ta hanyar tabbatar dashi, ma’aikatu da dama za su daina biya.

“Don haka, ya zama dole gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa an hukunta duk wanda yaki biya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel