Rashin iya mulki: Dan majalisa ya nemi gwamnan jigawa yayi murabus daga kujerarsa

Rashin iya mulki: Dan majalisa ya nemi gwamnan jigawa yayi murabus daga kujerarsa

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gumel, Gagarawa, Maigatari da Sule tankarkar a majalisar wakilai, Alhaji Sani Zorroye nemi gwamnan jahar Jigawa, Abubakar Muhammad Badaru daya sauka daga mukaminsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Zorro ya bayyana haka sakamakon zargin da yake yi ma gwamnan na cewa ya gaza mulkin jahar yadda ya kamata, bashi da gogewa a faggen mulki, kuma ya gaza wajen shawo kan miyagun laifuka a jahar Jigawa.

KU KARANTA: Zargin Buhari na barci akan aiki: fadar shugaban kasa ta mayar ma Fasto da martani

Rashin iya mulki: Dan majalisa ya nemi gwamnan jigawa yayi murabus daga kujerarsa

Badaru da Zorro
Source: UGC

Haka zalika Zorro ya zargi Gwamba Badaru da gayyato Chanisawa zuwa jahar Jigawa don su dinga bautar da jama’an jahar, ya kara da cewa zuwa yanzu gwamnan ya kai ziyara kasar China sau goma sha hudu, kum duk don biyan bukatunsa ne.

“Badaru ya baiwa kamfanin Chanisa kyautan hecta 20,000 na filayenmu ba tare da biyan wata gwaggwabar fansan da tayi daidai da darajar filayen ba, idan kuma jama’a suka nuna rashin amincewa ko suka yi korafi sai kaga ya dauresu.

“Badaru ya kwashe tsawon lokaci a kasar China yana kulla huldar kasuwancinsa, fiye da yadda yake kulla abinda zai amfani jahar Jigawa, a cikin shekaru uku da suka gabata ya tafi China sau 14, da haka gwamnan jahar Zamfara ya gurgunta jahar Zamfara.

“Ya tare a Abuja da sunan aikin kungiyar gwamnonin Najeriya, har yan bindiga suka mamaye jahar, yanzu gashi lamarin ya wuce gona da iri, bamu so hakan ya maimaitan kansa a jahar Jigawa, gashi yanzu gwamnan yafi zama a wajen Jigawa, kuma yan bindiga sun fara kai hare hare kauyukanmu. Don haka muke kira gareshi da yayi murabus kafin matsalar ta ta’azzara.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel